Abubakar Abba" />

Mun Ga Alfanunon Garkame Iyakokin Nijeriya, Cewar Kungiyar Manoman Citta

Kungiyar manoman Citta ta kasa ta bayyana cewa, kulle iyakokin kan tudu na kasar da Gwamnatin Tarayya ta yi a watannin baya, hakan ya kara bunsa noman Citta a daukacin fadin kasar.

A cewar kungiyar, hakan ya kuma kara bunksa nomanta da kuma kara samar da dimbin kudaden shiga ga manomanta dake kasar nan.
Bayanin hakan yana kunshe ne a cikin sanarwar da kungiyar ta fitar a babban birnin tarayyar Abuja, inda kungiyar ta kara da cewa, hakan ya kuma kara taimakawa wajen kara farfado da tattalin arznin kasar nan, musamman fannin noman Citta a kasar.
Sanarwar wacce shugaban kungiyar Haruna Abdulazeez, inda ya sa hannun, ta kuma koka kan halayyar wasu noman Citta a kassr nan wajen yin almundaha.
Ya nuna taikacinsa karara kan yadda wasu manoman Citta dake kasar nan basa son shiga cikin kungiyar don suma su zamo yayanta.
A cewarsa, kawai, daukacin manoman Citta dake a daukacin fadin kasar nan, da za su iya amfana da dukkan wani tallafi dake fitowa daga bangaren gwamnati, musamman Gwamnatin Tarayya.
Ya kuma gargadi daukacin yayanta dake a daukacin fadin kasar nan ka da su jefa kansu a cikin akaita dukkan wasu nau’uka na almundaha a cikin noman su na Citta, inda ya kara da cewa, abin takaici kan yadda wasu manoman Citta dake a kasar nan ba sa cikin kungiyar.
Ya yi nuni da cewa, rashin shiga kungiyar da wasu manoma basa son yi, ya bukace su dasu gaggauta yin ragista don a hada kai a samu ci gaba.
Shugaban Haruna Abdulazzez ya kuma yi kira ga daukacin ‘ya’yan kungiyar dake a daukacin fadin kasar nan su kasance masu yin gaskiya wajen noma Cittar da kuma sayar da ita a kasuwanni.
Bugu da kari, an kuma ruwaito Shugaban Shirin APPEALS na Jihar Kaduna Dokta Yahaya Aminu ya sanar da cewa, Kudancin Kaduna ne ya fi ko’ina noman citta a Afirka, inda kuma koka kan cewar, abin takaici ne duk da kasancewar Kudancin Kaduna ne ya fi ko’ina noman citta a Afirka.
A cewar shugaban Dokta Yahaya Aminu an kuma ittifaki cewa, tana daya daga cikin citta mafi kyau da daraja a duniya amma har yanzu sun gaza samar da abin da duniyar ke bukata saboda rashin bin hanyoyi da dabarun zamani.
Shugaban wanda ya sanar da hakan a hirarsa da nanema labaraia a Kaduna ya kuma yiwa manoman citta albishir kan shirin da Gwamnatin Jihar Kaduna da hadin gwiwar Kamfanin OCP da ke kasar Moroko ke yi don auna irin kasar da kowace karamar hukuma da yanki ke da shi don manoman su rika dubawa don sanin duk irin nau’in da kuma nau’i da adadin takin da za su yi amfani da shi a gonakinsu.
Ya kuma bayyana hasarar da ake yi wajen noman citta da ke farowa tun daga girbi har zuwa sauran dawainiyar da ake yi mata, inda ya ce hakan ya kan shafi inganci da yawan abin da ake nomawa maimakon bayar da shawarar dibar kasar zuwa dakunan gwaje-gwaje da suka yi karanci a Nijeriya, kuma hakan ke shafar noma a Nijeriya.
Dokta Yahaya Aminu Dokta Yahaya shirin bunkasa aikin noma da Inganta sarrafa kayan gona da ake kira ya taimakawa manoman citta da dama dake a cikin jihar, musamman don su kara bunkasa fannin, inda ya yi nuni da cewa, fannin yana taiakawa matuka wajwn samar da kudin shiga ga manoman citta da kuma kara habaka tattalin arzikin jihar.

Exit mobile version