Abubakar Abba" />

Mun Ga Canji A Noman Kwakwar Manja Karkashin Shirin Anchor Borrowers, Cewar Cif Igwe

Shirin Anchor Borrowers

Shugaban Kungiyar Manoman Kwakwar Manja ta kasa Cif Igwe Hiliary Uche ya sanar da cewa, Babban Bankin Nijeriya CBN ya zabi kungiyar don ta amfana a karshin shirin bayar ta tallafin aikin noma na Anchor Borrowers.

Shugaban ya ci gaba da da cewa, Babban Bankin Nijeriya CBN, ya zabi kungiyar don ta noma Kwakwar Manja ta musamman, inda ya kara da cewa, a yanzu kungiyar tana kan tattaunawa da r Babban Bankin Nijeriya CBN kan yadda za’a tunkari aikin.

A cewar Shugaban Kungiyar Manoman Kwakwar Manja ta kasa Cif Igwe Hiliary Uche, fasahar da ake da ita a kasar nan, ta karu matuka wajen sarrafa Kwakwar Manja ta musamman a cikin kasar.

Shugaban Kungiyar Manoman Kwakwar Manja ta kasa Cif Igwe Hiliary Uche ya yi amannar cewa, shirin zai taimaka matuka wajen kara daga tattalin arzikin kasar nan, inds ya kara da cewa, Babban Bankin Nijeriya CBN a yanzu, ne yake yin aiki da Manoman dake a cikin kasar nan wadada kuma suke samar da kimanin kashi 80 bisa dari na Manjan da ake yin amfani da shi a cikin kasar nan, inda ya sanar da cewa, akwai matukar wahala wajen iya tafiyar da Manoman Kwakwar Manja da ke a cikin karkara.

Shugaban Kungiyar Manoman Kwakwar Manja ta kasa Cif Igwe Hiliary Uche, a yanzu, kungiyar ta dora Manoman Kwakwar Manja kan turbar yin noman Kwakawar ta zamani, indanya kara da cewa, muna jihohi 24 da yau suke noman Kwakwar Manja, inda kuma a wasu jihohin, mana da tsari 18 na noman Kwakwar na zamani, wasu kima suna da uku wasu bakwai.

Da ya ke yin tsokacin Irin na Kwakwar Manja, Shugaban Kungiyar Manoman Kwakwar Manja ta kasa Cif Igwe Hiliary Uche ya ce, a cikin shirin Babban Bankin Nijeriya CBN zai baiwa Cibiyar gudanar da bincike kan fannin noman Kwakwar Manja kudi kai tsaye don samar ingantaccen Irin na Kwakwar Manja ga Manoman na Kwakwar Manja.

A cewar Shugaban Kungiyar Manoman Kwakwar Manja ta kasa Cif Igwe Hiliary Uche idan aka ci gaba da gudanar da shirin, zai taimaka wajen samar da ingantacciyar Kwakwar Manja, inda hakan kuma zai kara samarwa da Kwakwar Manja farashi mai kyau a kasuwanin duniya.

Shugaban Kungiyar Manoman Kwakwar Manja ta kasa Cif Igwe Hiliary Uche ya kara da cewa, umarnin da gwamnatin tarayyar ta bayar a watanin baya da suka shige na rufe iyakokin Nijeriya na kan tudu musamman matakin ya kara taimaka wa fannin noman Kwakwar Manja a kasar da kima su Manoman ganin yadda suka kara dukufa sosai wajen noman ta a kasar nan.

Shima wani Manomin na Kwakwar Manjan Paul Anza ya sanar da cewa, akwai dimbin arziki da Nijeriya za ta iya amfana a fannin na noman Kwakwar Manja, in har gwamnatin tarayya ta samar da ingantaccen tsari.

Manomin na Kwakwar Manjan Paul Anza ya kuma shawarci gwamnatin da ta kakkafa wuraren gudanar da bincike kan Irin na Kwakwar Manja tankuma kara tsaurara hana hana shigo da Kwakwar Manja cikin kasar nan ko da bayan an bude iyakokin Nijeriya.

Shi ma wani kwarre a fannin noman Kwakwar Manja Dakta Tunde Abayomi ya yi nuni da cewa, ya zama wajibi mahukunta a kasar nan suyi dubi da kyau kan irinnalfanun dake tattare da fannin na noman Kwakwar Manja a kasar nan, indanya yi nuni da cewa, wasu kasashen duniya da wannan fanninnne suke ciyar da tattalin arzikin su gaba, inda ya kara da cewa, noman Kwakwar Manja a kasar nan kadai ya isa ya samarwa da Nijeriya dimbin kudaden shiga masu yawa.

A wata sabuwa kuwa, kimanin manoma su miliyan 10 dake a daukacin fadin kasar nan ne suka amfana a karkashin shirin noma na Anchor Borrowers dake a karkashin kulawar Babban Bankin Nijeriya CBN.

Mataimakin Sakatare na kungiyar manoman Shinkafa ta kasa (RIFAN), Alhaji Iliyasu Awodi ne ya sanar da hakan a hirarar sa kamfanin dillancin labarai na kasa a Babban Birnin Tarayyar Abuja.

A cewar Mataimakin Sakatare na kungiyar manoman Shinkafa ta kasa (RIFAN), Alhaji Iliyasu Awodi manufar shirin shine, a sada kamfanonin aikin nomad a kananan manoman dake kasar nan yadda zasu samu amfanin gona mai dimbin yawa.

Mataimakin Sakatare na kungiyar manoman Shinkafa ta kasa (RIFAN), Alhaji Iliyasu Awodi ya sanar da cewa, manoman da suka amfana a karkkashin shirin musamman manomann Shnkfa, sun samu albarkar nona mai yawa ta hanyar shirin

Exit mobile version