Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Mun Gaji Da Kyankkyasa Rana Na Kashewa: Bambanci Tsakanin Mabarata Da Mabukata Batu Kan Matsalar Barace-Barace A Wannan Kasa.

by
2 years ago
in HANGEN NESA
5 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Labarai Masu Nasaba

Waiwaye Kan Ruɗanin Dake Cikin Babban Zaɓe Me Zuwa Na 2023

Rufe Iyakoki: Ina Kishin Kasa Ya Ke Ga ‘Yan Arewa?

A wannan gaba za a yi duba tare da yin tankade da rairaya a kan su wane ne almajirai mabukata da kuma su wane ne almajirai mabarata? Hakazalika za a yi duba tare da yin tsokaci a kan mene ne dalilin da ya sa ake yin bara, sannan za mu kalli mene ne matsayin almajiranci a tunanin Bahaushe?

Kalmar almajiri, kalma ce Balarabiya wadda aka arota daga harshen Larabci da take dauke da ma’anar Dan hijira, wato al-muhajir, mai hijira daga wani gari zuwa wani garin don neman karatu na Al-Kur’ani mai girma.
A lokutan baya kowa ya San cewa masu tafiya neman ilimi gabas suke tafiya, wato garuruwa irin su Maiduguri da Nguru da Pataskuma da Gashuwa da sauran manya-manyan garuruwa dake arewa maso gabashin kasarnan. A da Almajirai ba abin da almajiri ya sa a gaba face karatun da ya kawo shi, don haka nema za ka ga a mafiyawancin garuruwa baya ga babbar tsangaya da ake da ita Almajirai sukan je su gina abin da ake kira da kiskali wato ‘Yan rumfuna ne suke zuwa su gina a bayan gari, a nan ne za a je a yi ta kwama karatu har zuwa faduwar rana. A gefe guda kuma ga kayayyakin abincinsu da suke nomawa a gayaunakansu kamar su rogo da gyada da wake da walahan ko makani ko dankali da dai sauransu, ga manya garada kuwa har masara da su dawa da gero suke nomawa don siyarwa su biya bukatun gabansa da kudin, hakazalika ga dinkin huluna duk suna daya daga cikin irin sana’o’in Almajirai musamman garada, ga su manyan almajiran a wasu lokuta sukan fita sana’ar yankan farce a duk ranar Alhamis ko Juma’a, haka ga kananan kuma sukan fita yawan neman kudi a duk ranar Alhamis da juma’a ta hanyar sayar da ruwan alwala a masallatan juma’a da makamantansu. Kamar yadda muka sani, babbar matsalar Almajiri ita ce ta abinci don haka nema a zamanin baya ba a fiye zuwa karatun allo manyan birane ba sai kauyuka da karkara domin akwai yalwar abin da za a ci. Amma ko da a birananne a zamanin baya za ka ga kusan kowanne kolo ko titibiri yana da uwar-daki, wannan uwar dakin a nan zai rinka aikace-aikace ana ba shi abincin safe da rana da daddare, sannan duk ranar Alhamis da Juma’a shi ne ranar wanki da rubutun sha. Su kuma manyan garada daga makota ake kawo musu domin kowanne gida yana da masaki guda da yake warewa irin wadannan garadan. Daga baya Almajirai suka fara barar abinci ba ta kudi ba.
Saboda haka, a zahirin gaskiya Almajiri a baya mabukaci ne domin duk abin da zai yi na ya samu ya ci yana yi ne a kan bukata in bukatarsa ta biya karatunnan zai sa a gaba. Amma a yau da yawa a yau mabarata ne ba mabukata ba, domin akasari ba ruwansu da harkar karatun sai barace-baracen kawai suka sa a gaba.
Dalilan da ya sa barace- barace suka yawaita a yau
1. Talauci
2. Lalaci da mutuwar zuciya.
3. Fahimta bai-bai
4. Sakacin hukumomi da yi wa harkar neman ilimin karatun Kur’ani rikon ko in kula
Talauci, a zamanin baya iyaye da gaske suke kuma son Allah Ya sa suke kai ‘ya’yansu karatun Almajiranci, don haka Allah Ya kalli al’amarin Ya sa masa albarka, amma yanzu wadansu daga cikin iyaye suna turo ‘ya’yansu karatun allo ne don su zama ATM wato abin da ake sawa a mashin din cire kudi a dauki kudi, ma’ana dai suna aiko yaran ne ko don su rinka nema musu kudi suna aika musu inda suke. Da wannan ne za ka ga maimakon yaran in sun zo su tsaya karatu ziryan sai abin da ba a rasa ba, sai su buge da neman kudi da shiga cikin ayyukan banza da na masha’a tare da yaran gari fanddararru.
Lalaci da mutuwar zuciya, shi ma wani dalili ne da ya sa barace-barace suka yawaita musamman a kasar Hausa, a yau za ka ga ba bukata ba ce ta sa ake bara a’a sai don an mayar da ita Sana’a.
Hakazalika, wadansu iyayen tamore da wayo irin na banza ya kansa su tattaro su turo yaransu bara, alal misali mutum ne zai kara aure kuma ba dakin da zai saka amarya sai dakin ‘ya’yansa don haka sai ya tukudo yaran duniya da sunan karatun allo, amma a cikin zuciyarsa ba don Allah Ya yi ba. Wadansu iyayen kuwa suna turo ‘ya’yayyensu bara ne don su gujewa sauke nauyin da Allah Ya dora musu na ciyarwa da tufatarwa da tarbiyya da koya musu dabi’u kyawawa da kuma addini.
Fahimta bai-bai, har ga Allah wadansu daga cikin iyayen da suke turo ‘ya’yansu bara su dauka addini ce haka ma ita manya bara, kai har ga masu bayarwar, Wanda kuma ba haka ba ne, sai dai ma Iya cewa bara ga Almajirai na Allah da Annabi ma’ana wadanda suka fito karatun don bukatace ta a ci don a yi karatu ba a ci don a yi shikiyanci ba, hakan ta faru ne saboda sakacin hukumomi da masu ruwa da tsaki musamman na arewacin Nijeriya in matsalar bara tafi katutu, Wanda bayanin hakan zai biyo baya.
Ina mafita? Alal hakika Gwamnatoci da masu ruwa da tsaki na arewa har yanzu bacci suke yi ba su farka ba a kan abin da ya shafi arewa, don haka ne ma duk wani abu da yake zama barazana ta zaman lafiya da kwanciyar hankali sun tabbata a arewacin kasarnan, kama ga talauci, da jahilci da mutuwar zuciya da kashe-kashen rayuka babu gaira babu dalili fiye da kowanne yanki na wannan kasa a yau. Don haka a kan magance wannan matsala da ta zama alakakai a wannan yanki, dole sai Gwamnoni da masu ruwa da tsaki sun bi matakai kamar haka;
1. Kirkirar wata hukuma wadda za ta yi duba a kan yadda za a hana barace-barace da ragewa mutane radadin talauci da kuma ilmantar da su a kan illar bara a ruwa da mutuntaka ta Dan Adam.
2. Kirkiro wani asusu da zai rinka fita kasashen larabawa don tara kudaden da za a rinka tallafa karantun Alkur’ani a wannan yanki a karkashin malamai na addini masu tsoron Allah.
3. Shigar da makarantun allo cikin kasafin kudi na shekara-shekara don tallafa musu.
4. Hana kwararar Almajirai daga wannan jiha zuwa waccan, kowanne Gwamna ya ji da makarantun allon jahohinsa.
5. Tara malaman makarantun allon don yi musu semina da kuma tura su irin kasashen da suke da makarantun allon kamar su Sudan ko Misara don gano yadda aka zamanantar da makarantun allon a can
6. Shigo da masu hali don kafa gidauniya mai karfi mai magana da yun yankin baki daya don su taru su tallafawa wannan shiri na hana Almajirai masu karatu barace-barace, amma wadanda suka mayar da ita Sana’a sai gwamnati ta dau mataki a Kansu ta hanyar da ta dace bisa ingantaccen tsari ba na siyasa ba.
A takaice maganar hana bara a wannan yanki na arewa alhakin ne na su Kansu al’ummar baki daya kama ga hukumomi da masu kudi da malamai da sauran al’umma, in ba haka, barazanar da ke tunkarar wannan yanki ta fuskar tsaro babba ce kwarai. In kune ya ji, dole gangar jiki ta yi aiki sai jiki ya tsira, amma kuma in an ki ji, ba a ki gani ba, in ko an gani, ba a ga da kyau ba.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Tarihin Rayuwa Da Al’adun kabilar Rabari

Next Post

Matsalar Rashin Haihuwa Da Maganinta (II)

Labarai Masu Nasaba

Waiwaye Kan Ruɗanin Dake Cikin Babban Zaɓe Me Zuwa Na 2023

Waiwaye Kan Ruɗanin Dake Cikin Babban Zaɓe Me Zuwa Na 2023

by
2 years ago
0

...

Rufe Iyakoki: Ina Kishin Kasa Ya Ke Ga ‘Yan Arewa?

by
3 years ago
0

...

Kalubalen Da Suke Gaban Sabon Editan BBC Hausa (III)

by
3 years ago
0

...

Kalubalen Da Suke Gaban Sabon Editan BBC Hausa (II)

by
3 years ago
0

...

Next Post
Matsalar Rashin Haihuwa Da Maganinta (II)

Matsalar Rashin Haihuwa Da Maganinta (II)

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: