Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home RIGAR 'YANCI

Mun Gamsu Da Ayyukan Dan Majalisar Wakilai Na Suleja – Inijinya Kabiru

by Muhammad
March 8, 2021
in RIGAR 'YANCI
2 min read
Suleja
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Muhammad Awwal Umar,

An bayyana cewar irin rawar da dan majalisar wakilai na tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Suleja, Tafa da Gurara, Hon. Abubakar Abdullahi Lado, ke gudanarwa ayyuka ne na cigaban kasa da tarihi ba zai manta da su ba.

Sakataren kungiyar Lado Support Organisation ta jiha, Injiniya Kabiru Abdulhamin Tungan Makama ne ya bayyana hakan a minna bayan kammala wani taron kungiyar da ta gudanar asabar din makon jiya a Minna.

Engr. Kabiru ya cigaba da cewar lallai Hon. Lado ya nunawa duniya cewar talakawa suka zabe shi dan bai watsa masu kasa a ido ba, ya gudanar da ayyukan da matasa kuma talakawa za mu yi alfahari da su a wannan kananan hukumonin da ba za mu manta da su ba.

Yanzu haka bisa kididdiga ya gudanar da ayyuka dari da ashirin da bakwai wadanda an kammala su kuma muna cin moriyarsu, tun farko mun tsaya tsayin daka dan ganin wakilce mu a majalisar kasa duk da kalubalen da muka fuskanta a baya, amma yau ba dan yankin mu ba kawai a jihar nan Hon. Lado abin a yaba ne domin duk ayyukan da ya gudanar na raya kasa da ma wadanda ake gudanarwa yanzu hakan wanda talaka zai yi na’am da su ne, muna goyon bayan shi kuma muna tare da shi domin ba mu zabin tumun dare ba.

Siyasar Lado ba ta ubangida ko dan wane ba ne siyasa ce ta karamta talaka dan yayi alfahari da abinda ya zaba. Yankin na tun dawowar siyasa 1999 ba mu zabi dan majalisar da ya taka rawar gani kamar Hon. Lado Suleja ba wajen yin tsayin daka dan sharewa talaka hawaye na ganin ya mori mulkin dimukuradiyya yadda ya kamata ba.

Ina jawo hankalin matasa, mata da sauran al’umma da mu cigaba da marawa Lado baya, domin wakilcin jama’a a irin wannan kujerar sai jarumi wanda yasan darajar amana da kulawa da alhakin da aka dora mai.

Mu a kananan hukumomin Suleja, Tafa da Gurara ba mu yi zaben tumun dare ba, za mu cigaba da goya baya da yin addu’o’in alheri gare shi dan samun nasarar sauke nauyin da ya rataya a wuyan shi.

SendShareTweetShare
Previous Post

Makarantar Madarasatul Ilmu Nuru Wa Dake Lokoja Ta Yi Bikin Saukar Alkur’anin Dalibai 17

Next Post

Ilimi: Jakadan Kasar Masar a Nijeriya Ya Yi Alkawarin Hada Hannu Da Gwamnatin Kano

RelatedPosts

Zamfara

Gwamnatin Jihar Zamfara Ta Tabbatar Da Kama  Wasu Sojoji Masu Hulda Da ‘Yan Ta’adda

by Muhammad
3 days ago
0

Daga Hussaini Yero, Gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da rahotan...

Kansila Mai Mataimaka 18 Ya Sadaukar Da Albashinsa Na Farko

by Sulaiman Ibrahim
3 weeks ago
0

Daga Abdullahi Muh’d, Kano Shugaban Gidauniyar ‘Charity’ mai rajin tallafa...

APC

Sanata Al-Makura Ya Cancanci Rike Kujerar Shugabancin APC, Inji Gwamna Sule

by Muhammad
3 weeks ago
0

Daga Zubairu M Lawal, A yayin da uwar jam'iyyar APC...

Next Post
Masar

Ilimi: Jakadan Kasar Masar a Nijeriya Ya Yi Alkawarin Hada Hannu Da Gwamnatin Kano

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version