Bala Kukuru" />

Mun Gamsu Da Mulkin Shugaba Muhammdu Buhari, inji Alhaji Shafi’u

Wani kodineto a karkashin inuwar Jamiyar APC wanda yake shugabancin hada kawunnan al’ummar kudu da kuma yammacin Nijeriya Alhaji Shafiu Danazumi Tofa kuma Sarkin kudun Agege wanda yake zaune a ungunwar Agege ta jihar Legas ya bayyana cewa, a halin yanzu al’ummar Nijeriya suna kara samum ci gaba tare da gamsuwa a wajen mulkin shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari a duk fadin kasar nan.
Alhaji Shafiu Danazumi Tofa ya yi wannan kalami ne jim kadan bayan kammala taronsa da wadansu ayarin ‘yan siyasa da suka fito daga sassa daban daban na jihar Legas a lokacin da yake zantawa da wadansu wakailan kafofin yada labarai a ofishinsa da yake Agege.
Taron wanda ya kunshi Hausawa da Fulani Da Yarabawa da barebari da Igala da sauran wadansu kabilan Arewacin Nijeriya mazauna jihar Legas da kewayenta baki daya
Taken wannan taro inji shi, shi ne neman karin hadin kan duk wani dan arewacin Nijeriya mazaunin jihar Legas domin zama tsintsiya madaunrinki daya kuma a cidgada dayin magana da murya daya da bayar da shawarwari masu ma’ana domin samun nasarar kada kuria lami lafiya a lokacin zabe mai zuwa.
Ya kara da cewa dan arewa an sanshi a duk inda yake zaune mutun ne mai kawaici da kaucema tashin hankali da kare mutuncinsa dana addininsa da sauran makamantansu, a kan haka ‘yan arewa mazauna Legas dana sauran wadansu jihohi da su ci bada da rikon wannan akida tare da zama a kan turbar gaskiya domin samun nasarorin gudanar da harkokin rayuwa a kowane lokaci ya kuma yi fatan Allah ya ci gada da yi wa shuwagabanni ja goranci na al’amuransu na yau da kullum.

Exit mobile version