Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Gwamna Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana cewa suna gamsuwa da yadda kamfanonin da ke aikin hanyoyi a Jihar Katsina kamar yadda aka yi yarjejeniya da su, tun kafin a ba su wannan kwagila.
Alhaji Aminu Bello Masari ya faɗi haka ne a lokacin da ya kai ziyarar aikin duba hanyoyin da Gwamnatinsa ta bayar da kuma wanda suka tarar amma suke yi domin cika alƙawarin cigaba da su don ganin an kammala su cikin ƙanƙanin lokaci.
Tun da farko Gwamna Aminu Bello Masari tare da tawagar majalisar zartawa sun fara kai ziyarar duba aikin sabuwar hanyar da ta tashi daga birnin Kuka zuwa Sankaya, wanda wannan Gwamnatin ce ta bada aikinta.
Kazalika Gwamna tare da ‘yan tagawar ta su sun duba akin aikin hanyar da ta tashi daga kwanar Sandamu zuwa garin Baban Mutun da ke iyaka da jihar Jigawa wanda tsohuwar Gwamnati ta fara amma dai wannan Gwamnatin ta ƙarasa aikin mai kilmanin kilo mita 44.
Kwamishinan ma’aikatar Ayyuka na jihar Katsina, Honorabul Tasi’u Ɗahiru Ɗanɗagoro ya ce wannnan hanyoyi sun yi alƙawarinsu ne a lokacinn da suke neman a zaɓe su, to gashi yau an fara cikawa inda aka kammala wasu, sauran kuma ana cigaba da aikinsu.