‘Mun Gamsuwa Da Jagorancin Mai Takobi A Kungiya Direbobi Ta ‘Imfuloya’ Ta Kasa’

Takobi

Daga Bala Kukkuru

shugaban kungiya masu motocin haya da dauka maikata  ta kasa na shiyar Jihar Kano wadda a kafi sani ta da sunan ta ‘Road Transport Employers’ Alhaji mustafha Jibrin Jabson Kano ya bayyana cewar shi da sauran shuwagabanni da mambobin kungiyar su na Jihar Kano dama Nijeriya baki daya suna cigaba da gamsuwa tare da gani a kasa a wajen jagorancin shugaban kungiyar ta kasa, Alhaji Musa Mohammed Mai Takobi a duk fadin kasar nan. Shugaban kungiyar Jihar Kano Alhaji Mustapha Jibrin Jibson Kano ya yi  wannan tsokacin ne a ofishin kungiyar dake Kano jim kadan bayan kamala taron su da wadansu kusoshin kungiyar a Jihar Kano, kuma ya bayyana wa LEADERSHIP HAUSA gaskiyar al’amarin.

A yayin da Alhaji Mustafha Jibirin Jabson Kano ya cigaba da cewa, babu shakka shugaban kungiya a matakin kasa baki daya Alhaji Musa Mohammed Mai Takobi Kano yana taka rawar gani a wajen jagoracin kungiyar a cikin watanni takwas (8) kacal da Allah ya bashi shugabancin kuginyar ta kasa, ya ce, amma a halin yanzu kungiyar ta kara samun  cigaba kwarai da gaske, don ta sanmu offishin ta na zama dindindin a birinin Abuja tare da mallakar babbar sakateriya wanda a cewar sa suna nan suna shirye shirye  kiran taron budeta a watan Janairu na shekara mai zuwa,

Mustafha Jibirin Jabson Kano ya  cigaba da shawatar fasinjoji masu ra’ayin shiga motocin haya a wajen tasha dasu kaucema hawa motocin haya a haramtatun wurare domin kare rayukasansu da lafiyar su.ak

Exit mobile version