Mun Gano Hanyoyin Da ‘Yan Bindiga Ke Samun Kudadensu -Gwamnatin Jihar Kaduna

Kudadensu

Daga Ibrahim Ibrahim,

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El Rufa’i, ya fallasa wurin da miyagun ‘yan bindiga da suka addabi jihar ke samun kudaden shiga.

Daga cikin hanyoyin samun kudinsu kamar yadda gwamnatin jihar ta ce shi ne, wurin karbar kudin fansa daga ‘yan’uwan wadanda suka sace da sauran cuwa-cuwa da kayayyakin haram.

Wannan na kunshe ne a rahoton tsaro na watanni uku da kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ya mika wa gwamnatin jihar da kuma manema labarai.

Rahoton ya lissafo sauran hanyoyin da kudi ke shigo musu da suka hada da siyar da dabbobin sata, ribar cinikayyar makamai da kuma bayar da hayar makamai ga wasu kungiyoyin ta’addanci.

A cewar rahoton, “Wasu kungiyoyi na bayar da hayar makamai ga kungiyoyin da ba su da shi, kuma su raba kudin da suka samu wurin ta’addanci.  Sauran hanyoyin samun kudin sun hada da harajin dole da suke kallafa wa manoma a kan gonakinsu.”

Rahoton ya kara da bayyana cewa, sukan bai wa masu kai musu bayanan sirri jari domin kasuwanci wanda suke aika musu da ribar. Ya kara da cewa yadda ‘yan bindigan ke kashe kudin ta hanyar siyan bindigogi, makamai da abinci.

Sauran sun hada da kudaden kaiwa da kawowa, magani, siyan kayan shaye-shaye, biyan masu kai musu bayanan sirri, kafafa kasuwanci wanda masu kai musu bayanai ke yi da kuma kai wa bokaye kudi domin nasarar ayyukansu.

Exit mobile version