Yusuf Shuaibu">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home TATTALIN ARZIKI

Mun Gano Kudaden NHIS Naira Biliyan Biyar Da Suka Bace – Sambo

by Yusuf Shuaibu
December 17, 2020
in TATTALIN ARZIKI
2 min read
Kudaden NHIS
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Sakataren hukumar inshoran lafiya ta kasa, Farfesa Nasir Sambo, ya bayyana cewa, hukumarsa ta gano kudaden da suka bace na naira biliyan biyar da suka wabe. Haka kuma ya bayyana cewa, hukumar NHIS ta samu damar dawo da wasu kudade da suka bace. Sambo ya bayyana hakan ne lokacin da yake gabatar da jawabi wajen taro matsalolin tattalin arziki a bangarorin lafiya da kulawa da wasu dubaru karo na 16, wanda ya gudana a Jihar Legas ranar Talata.

Ya ce, “Sauran abubuwan da muka yi dai sun hada da samun damar farfado da hanyoyin kudade a kan inshoran lafiya a hukumar NHIS.

samndaads

“Lokacin da na zama sakataren shirin insharan lafiya, biliyoyin kudade sun bace ba tare da wani dalili ba.

“Mun samu nasarar fitowa daga wannan matsala ta hanyar bin ofishin akawun gwamnatin tarayya da hukumar yaki da cin hanci da rashawa wanda muka hada hannu da karfe, inda muka sami nasarar dawo da kudade har na naira biliyan biyar wanda suka bace a hukumar NHIS.

“A lokacin da muka sami wadannan kudade, ina mai tabbacin za a samu gagarumin canji a hukumar NHIS,” in ji shi.

Ya ci gaba da bayyana cewa, kididdiga ya  nuna cewa sama da mutane miliyan 82.9 ke fama da matsanancin talauci, kamar  yadda hukumar kididdiga ta kasa ta bayyana a shekarar 2019.

Haka kuma, Bankin Duniya ya kimanta cewa, ‘yan Nijeriya miliyan 92.6 za su kasance cikin mummunan talaauci a shekarar 2022.

Ya ce, “talauci yana karuwa ne idan ya kasance an samu karancin samun lafiya ga talakawa.

“Hukumar kula da cutattuka ta kasa ta bayyana cewa, ana samun karuwar cutattuka a Nijeriya wadanda suka hada da zazzabin cizon sauro da kuma  cutar Korona wanda ake fama da ita a halin yanzu.”

Ya kara da cewa, duk da wadannan abubuwan, Nijeriya tana iya bakin kokarin wajen bunkasa harkokin lafiya a karkashin shirin nan na cimma muradu na shekarar 2030. Ya ce, gwamnatin Nijeriya tana daukan matakan da suka dace wajen farfado da harkokin lafiya a cikin kasar nan musamman ma a yankunan karkara wanda ake samar da magunguna da cibiyoyin  lafiya da samar da kayayyakin lafiya na zamani.

SendShareTweetShare
Previous Post

Bankin Duniya Da IMF Sun Amince Wajen Bai Wa Nijeriya Bashin Biliyan Dala 11.465

Next Post

Yadda Za A Rage Karancin Abinci A Nijeriya Daga Kwararre

RelatedPosts

Lantarki

Bangaren Lantarki Ya Tafka Asarar Naira Biliyan 20.5 Saboda Karancin Gas

by Yusuf Shuaibu
22 hours ago
0

Bangaren wutar lantarki a Nijeriya ya tafka asarar harajin naira...

Matsalolin

Masana Sun Bayyana Hanyoyin Da Nijeriya Za Ta Bi Wajen Dakile Matsalolin Tattalin Arziki

by Yusuf Shuaibu
22 hours ago
0

Masana harkokin kudade da na tattalin arziki sun bukaci gwamnati...

Tattalin arziki

Yadda Ta’addanci Ya Lakume Tattalin Arzikin Dala Miliyan 80 A Arewa – Buhari

by Yusuf Shuaibu
22 hours ago
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta...

Next Post
Karancin Abinci A Nijeriya

Yadda Za A Rage Karancin Abinci A Nijeriya Daga Kwararre

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version