Abba Ibrahim Wada" />

Mun Hakura Da Lashe Gasar Firimiya – Klopp

klopp

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Jurgen Klopp, ya bayyana cewa rashin nasarar da sukayi a hannun kungiyar kwallon kafa ta Leceister City ranar Asabar yasa sun hakura da neman sake lashe gasar firimiya ta bana kuma zaiyi kokarin ganin sun kammala firimiya a cikin ‘yan hudun farko

Leicester City ta koma matsayi na biyu na wucin gadi a teburin Premier bayan ta doke Liverpool 3-1 a karawar da suka yi ranar Asabar a filin wasa na King Power, wasan da yabawa magoya bayan kungiyar Liverpool mamaki.
Liverpool ce ta fara cin kwallon inda inda dan wasa Muhammad Salah ne ya fara bude raga ana minti 67 da fara wasa amma kuma a minti na 78 dan wasan tsakiyar Leceister City James Maddison ya farke wa a bugun tazara.
Jagoran kungiyar bardy da matashin dan wasa Barnes ne suka ci wa Leicester City sauran kwallayen a ragar Liverpool cikin minti takwas kuma yanzu Leicester City tana da maki 46 tazarar maki bakwai tsakaninta da Manchester City wadda ta karbi bakuncin Tottenham kuma ta lallasa ta daci 3-0 a filin wasa na Ettihad duka a ranar ta Asabar.
“Tabbas wannan rashin nasarar ya tabbatar min da cewa ba zamu iya lashe gasar firimiyar Ingila ba ta bana duk da cewa mune yakamata mu kare kambu amma halin da tawagar mu take ciki yasa dole mu hakura” in ji Klopp
Ya kara da cewa “Abubuwa sun canja mana lokaci daya wanda kuma idan muka duba zamu ga cewa suna da alaka da ciwon da ‘yan wasa suka tafi da kuma gajiyar da ‘yan wasan sukayi suna buga wasa”
Liverpool mai rike da kofin gasar kuma tana nan a matsayi na hudu da maki 40 tazarar maki 13 tsakaninta da Manchester City bayan da tawagar ta Guardiola ta lallasa ta Mourinho daci 3-0 a ranar Asabar din.

Exit mobile version