Mun Hakura Da Lashe Gasar Firimiya –Klopp

Klopp

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liberpool, Jurgen Klopp, ya bayyana cewa yanzu ya hakura da sake lashe gasar firimiyar bana kuma zasu mayar da hankali wajen ganin sun kammala kakar bana cikin kungiyoyin hudun farko.

Manyan kusukure biyu da mai tsaron ragar Liberpool Alisson Becker ya yi sun taimaka wa Manchester City dura kwallo har hudu a ragar zakarun na Premier League a wasan mako na 23 da suka buga a filin wasa na Anfield kazalika, kungiiyar ta Guardiola ta bayar da tazarar maki biyar a saman teburin gasar.

Dan wasan Jamus, Gündogan ne ya fara zira kwallo a minti na 49 bayan ya zubar da finareti kafin a tafi hutun rabin lokaci sakamakon ketar da Fabinho ya yi wa Sterling sai dai Mohammed Salah ya farke wa Liberpool a minti na 63 daga bugun finareti kafin daga bisani Sterling da Foden su kara ta uku da ta huɗu.

Yanzu haka akwai tazarar maki 10 tsakanin Manchester City a saman teburi da kuma Liberpool a mataki na hudu bayan wasan da aka buga a Anfield kuma Chelsea wadda ta doke Sheffield United ta koma mataki na biyar.

Exit mobile version