Connect with us

LABARAI

Mun Kafa Kwamitin Da Zai Duba Batun Karkatar Da Kudaden Tsaro A Katsina – Gamayyar Jam’iyyu

Published

on

Hadadiyar gammayar jam’iyyun adawa masu bada shawara a kan al’amuran da suka shafi gwamnati da kuma al’umma da ake kira ‘Inter-party Adbisory Council IPAC  a turance, ta kafa wani kwamiti akan zargin da wani Dan Kasuwa Mahdi Shehu da ya yi akan gwmanati jihar Katsina na karkatar da kudacdan tsaro.

Dan kasuwar dai ya yi zargin cewa gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin gwamna Aminu Bello Masari sun banzatar da kudadan jihar da aka ware domin tunkarar matsalar tsaro har naira biliyan 52 zargin da gwamnati ta ce wannan maganar babu gaskiya acikin ta.

Bisa wannan dalili ne yasa wannan gammayar kungiyar jam’iyyun adawa suka rubuta takarda suka aikawa gwamnatin jihar Katsina domin a ba su hujjujin da gwamnati ta dogara da su na karyata zargin da Alhaji Mahdi shehu ya yi masu.

Haka kuma sun rubuta irin wannan takarda zuwa ga hamshakin dan kasuwar Alhaji Mahdi shehu inda suka bukaci da ya ba su hujjuji a rubuce domin su yi nazarin kowane bangara kafin su dauki matsaya akan wannan batu.

Shugaban gammayar kungiyar jam’iyyun adawa a jihar Katsina, Alhaji Ibrahin Tukur Saude ya bayyana haka ga manema labarai a Katsina inda ya kara da cewa sun ba kowane bangare awa 48 domin a ba su bayani abinda suka bukata a rubuce kafin daukar mataki na gaba.

Alhaji Ibrahim Tukur Saude ya kara da cewa kafin su yanke wannan hukunci sai da suka y wani taron gaggawa inda shuwagabanin jam’iyyu goma sha shida da suke da rijista a Najeriya kuma suke da wakilci a jihar Katsina, bayan cimma matsaya ne suka rubuta takardun daban-daban

“Batun wannan zargin da Mahdi Shehu ya yi wa gwamnatin jihar Katsina, muna da rawar da zamu taka ta tsaka-tsaki domin ganin an samu warware wannan matsala da ta ta so, ba tare da wata wahala ba” in ji shi
Advertisement

labarai