Connect with us

RIGAR 'YANCI

Mun Karbo Sama Da Naira Miliyan Shida A Hajji Camp – Auwalu Shinkafi

Published

on

Alhaji Auwalu Ahmad Shinkafi, Shugaban kungiyar ’yan kasuwar sansanin alhazai da ke Kano ya bayyana cewa, daga hawansa shugabancin kungiyar shi da masu taimaka ma sa yanzu haka ya samo nasarar karbo kudaden ’yan kasa kimani sama da Naira Milliyan dhida bisa taimakon masu shari’a ko sulhuntawa a wannan kasuwa ta Hajji Kam da ke Kano, ya na mai cewa, wannan nasara ce babba da ba a samu a baya ba.

Alhaji Auwalu Ahamad Shinkafi ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke jawabi bayan kammala taron da ’yan kungiyar su ka yi kan kokarinsu na yakar annobar cutar Korona a kasuwar.
Haka kuma ya ce, ba shakka kulle da a ka yi na kasuwanni an samu matsala, inda mafiya yawan ’yan kasuwa sun cinye jarinsu, ya na mai cewa, idan kana da jarin Naira 500,000 ta koma Naira 100,000 ko kasa da haka.
Har ila yau, ya nemi tallafin Gwamnatin Kano da kasa kan wannan masifa da a ka samu kai a ciki, domin su da ma a can baya sun yi gobara, wacce su ka yi asara mai yawa a kasuwar, amma dai ba su sami wani taimako ba. Don haka su na bukata a yanzu, kamar yadda a ka yi wa wasu a baya, su ma a ba su.
A karshe dai ya ce, shi da mataimakansa irinsu sakataren kungiya Aminu Bin Mu’allim da mataimakinsa Abdulkadir Adamu Magyazo da jami`in yada labarai Aminu Boku Gama da kuma mataimakin sakatare Musa Doron Kudi da mai binciken kudi Alhaji Lawan da kuma shugabar mata Hajiya Adama Wada sun nuna gamsuwa da tsarin wannan kungiya da kuma yadda a ke ba wa Gwamnan Kano Dr Abdullahi Ganduje goyan baya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: