Yusuf Shuaibu" />

“Mun Kashe Tsohon Dan Majalisar Anambra Ne Don Ya Hana Ayyukan ’Yan Kungiyar Asiri”

Wani dan kungiyar asiri mai suna Chigbo Aniegbu, wanda ake zargin yana da hannu a kisan tsohon dan majalisar Jihar Anambra, Frank Igboka, ya bayyana cewa kungiyar sa ne ta kashe dan majalisar domin ya hana ayyukan kungiyar a yankin Nimo. Lokacin da aka gurfanar da shi a shalkwatan ‘yan sanda ranar Litinin, wanda ake zargin mai shekaru 27, ya bayyana cewa Igboka ya matsa wa kungiyarsa a yankin Nimo.
Aniegbu wanda ake yi wa lakabi da Transformer, ya zargi mamacin da cin alwashin kar a sake a bar kungiyar nasu dawowa cikin yankin har sai in sun daina gudanar da ayyukansu. Sunan kungiyarmu ‘Bikings Cult’, ya musanta yana da hannu a cikin kisan Igboka. Ya ce, “Ina yankin Oyeolise lokacin da ‘yan kungiyarmu suka nemi in bi su zuwa gudanar sintiri, amma na ce musu ba zan shiga cikin wadanda za su kashe Igboka. Na firgita kwarai lokacin da suka kashe tsohon dan majalisar.”
Kwamishinan ‘yan sandar Jihar, Mustapha Dandaura, ya bayyana cewa sauran ‘ya’yan kungiyar guda uku sun gudu. Ya kara da cewa, a yanzu haka ana kokarin yadda za a samu nasarar cafke dukka sauyan ‘yan kungiyar. Kwamishinan ya bayyana sunayen ‘ya’yan kungiyar wadanda suka gudu kamar haka Chukwunonso, Nwasami da kuma Obinna Okafor. Ya ci gaba da cewa, gwamnan Jihar Willie Obiano, ya yi alkawarin bai wa duk wani mutum wanda ya bayar da bayani wanda zai kai ga cafke dukkan wadanda suke da hannu a wajen kisan tsohon dan majalisar Jihar, daga naira miliyan biyar har zuwa naira miliyan 10 zai iya ba shi.
Ya ce, “Ina farin cikin da gwamna ya kara kudin da zai bai wa duk wani mutum da ya bayar da bayanai da za su kai ga cafke sauran mutum uku a kan naira miliyan biyar ga kowani mutum daya. “Idan za a iya tunawa dai, a ranar 16 ga watan Afrilun shekarar 2019 da misalin karfe 8.18, wasu ‘yan bindiga suka harbe shugaban yankin Nimo, Cif Frank Igboka, har lahira a kasuwar Nimo cikin karamar hukumar Njikoka ta Jihar Anambra. “Bayan aukuwar lamarin, rundunar ‘yan sandar sun kaddamar da barautar wadanda suke da hannu a cikin wannan mummunar aika-aika, wannan ne ya kai ga cafke Chigbo Aniegbu wanda ake yi wa lakabi da Transformer. Ana kokarin cafke sauran ‘ya’yan kungiyar wadanda suka guda, tare da kokarin gurfanar da su a gaban shari’a.”
Ya siffanta watan Afrilu a matsayin wata mai albarka, bisa yadda rundunarsa ta samu nasarar cafke masu laifi da dama a cikin watan. Dandaura ya bayyana cewa, sun samu nasarar cafke wadanda ake zargi da aikata laifu guda 265 a cikin watan Afrilu.

Exit mobile version