Connect with us

TATTAUNAWA

Mun Koya Wa  Matasa Fiye Da 15,000 Sana’o’i Kyauta — Adama Shekh Ali

Published

on

A shirin da wasu kungiyoyi masu zaman kansu su ka sa a gaba na ganin sun tallafa wa matasa maza da kuma mata da sana’o’in dogaro da kai, domin tserar da matasan daga gungun ’yan zaman kashe wando, za mu iya cewar gidauniyar Ajoke Ayisata Afolabi Foundation, wacce ke Unguwar Na-Shuka Hanwa a karamar hukumar Sabon Garin Zariya ta ciri tuta kan abubuwan da ta saka a gaba, domin inganta rayuwar matasan da su ke sassan karamar hukumar ta Sabon Gari da wasu kananan hukumomi a Jihar Kaduna.

Wakilin LEADERSHIP A YAU, ISA ABULLAHI GIDAN BAKKO, ya sami damar zantawa da babbar dan yatsa a wannan gidauniya mai suna HAJIYA ADAMA SHEKH ALI. Ga kuma yadda wannan tattaunawa tasu ta kasance:

 

Hajiya, Ya a ka yi wannan gidauniya ta kafu?

An kafa wannan gidauniya ce a watan Yunin shekara ta 2014, wato a yau zan iya cewar mu na da shekara shida ke nan da fara ayyukan tallafa wa al’umma ta koyar da su sana’o’in dogaro da kai da sauran tallafi mai yawan gaske. Kuma bawan Allah da ya kafa wannan gidauniyar, a Ikko wato jihar Legas ya ke zaune, kuma babban likita ne, kafin mahaifiyarsa ta rasu ita mahaifiyarsa, babban aikin da ta ke yi shi ne tallafa wa al’umma ta ko wane bangare da al’umma ke bukata, kafin ta rasu ta bukace shi da idan ta riga shi rasuwa, ya kafa wata gidauniya da za ta zama sadaka mai gudana domin ta, bayan mahaifiyarsa ta rasu, sai ya ci gaba daga inda ta tsaya na batun tallafa wa al’umma na kusa da na nesa, kuma wannan gidauniya ta mu, babbar cibiyar tan a Ikko,a yankin  Ibeda a karkashin wannan bawan Allah.

Shi wannan bawan Allah abokin mai gida na ne, sai wata rana ya ce wa maigidana, ya na son bude wannan gidauniya a arewa, amma matsalar ba shi da wanda ya sani da zai kula da ayyukan gidauniyar, kan haka sai mai gida na ya ce, ai mata ta za ta iya rikewa, domin tan a da ilimin zamani, hart a kai ga kammala digirin tan a biyu a shekara ta 2008, sai ya ce wa wannan bawan Allah, babu ko shakka mata ta za ta iya rike ma ka wannan gidauniyar, tare da aiwatar da duk abin da ka ke son aiwatarwa, kuma ma a kafa wannan gidauniyar, ni tare da mai gida na mu na tallafa wa al’umma ta bangarori da dama, da suka hada da tallafa wa al’umma da abinci da kula da lafiyarsu da kuma biya wa ‘ya’yan talakawa kudin makaranta na ko wane mataki na ilimi, to da wannan gidauniya ta samu, aka kuma sa ni in zama shugabar gidauniyar bisa amana, ba wani sabon abu ba ne ya zo gareni tare da mai gida na, kuma duk ayyukan tallafa wa al’umma da mu ked a mai gida na, da mu kwashe shekaru mu na yi, ba a karkashin wata gidauniya ce mu ke yi ba, saboda haka, a lokacin da aka samar da wannan gidauniya, sai mu ka fadada ayyukan da mu ke yi daga na kusa da mu, mu ka fadada ayyukan ta ga al’umma, mabukata.

Da aka bude wannan gidauniya, wasu ayyuka ku ka sa wa gaba da suka shafi tallafa wa al’umma?

Da farko, mun zakulo marayu da iyayensu maza suka rasu, mu na  kula da iliminsu da abin da zak su cid a kuma tallafa wa iyayensu wajen biya ma su kudin makaranta, kamar yadda nabayyana ma ka abaya, amma da mu ka ga nasarorin da mu ke samu na ci gaba, sai mu ka fara koyar da marayun sana’o’in dogaro da kai, kamar yin takalma da  da yin jaka da yin man shafawa da kwamfuta da dunkin keke da saka  dai sana’o’in dogaro da kai da yawan gaske, mun yanke hukumcin samar da sana’o’in ga marayun da kuma yaran marasa karfi ne, domin samun damar yadda za su dogara da kansu ako wane lokaci, ba sai sun dogara da tallafin da aa’umma ke ba su ba.

Na wa ake sayar da takardar shiga wannan cibiya?

Kamar yadda na bayyana ma ka, wannangidauniyar an kafa ta ne domin tallafa wa marayu da sauran al’umma, saboda aka, wannan gidauniya ko da da rana guda, ba a taba sayar da takardar neman shiga wannan gidauniya ga duk mai bukatar koyon sana’a ba, komi kyauta ne mu ke bayar wa ga marayu da sauran wadanda ke cikin gidauniyar.

 

Za ki tunawa ko kunfara da marayu da mabukata koyon sana’a nawa a wannan gidauniyar da ki ka ce, kun fara a shekara ta 2014?

Zan iya tunawa mun farad a marayu hamsin maza da mata da suka fito daga sassan karamar hukumar Sabon gari da Giwa da Kudan da Soba da kuma karamar hukumar Zariya, amma kuma zuwa yau d azan iya cewar, shekar shida ke nan da bude wannan gidauniya, mun koya wa matasa maza da matasa marayu da ‘ya’yan marasa karfi sana’o’in dogaro da kai fiye da dubu goma sha biyar da suka fito daga sassan da na bayyana a baya.

Ga wadanda suka kammala koyon sana’o’I a karkashin wannan gidauniyar, in sun yi wasu abubuwanda suka koya a wannan gidauniyar, kun a ma su hanyar da za su sayar?

Babu shakka da mu na yi ma su hanyar tare da ba su tallafin kayayyakin da za su ci gaba da yin sana’o’in da suka koya, sai mu ka fahimci, wasu ba su da gaskiya, in mun basu tallafin sai mu wayi gari mu yi tozali da abin da mu ka ba su, domin ci gaba da sana’ar a kasuwa, kamar keken dunki da dai sauransu, wannan ya sa duk wannan ya kammala koyon sana’a, mu kan bas hi shawarar yadda zai ci gaba da yin sana’ar day a koya.

Wani abu ma da mu ke yi wa wadanda ke koyon sana’o’in, duk abin da mai koyo ya hada a cikin wannan gidauniya, na shi ne, ban a gidauniya ba ne, abin nufi shi ne, in mai koyon sana’ar ya yi tattali da amfani da shawarwarin da mu ke ba su, a dan lokaci kadan zai ga canjin rayuwa na samun rayuwa mai kyau a cikin sauki. A wasu lokuta ma, in wadanda mu ke koyar da su sana’o’in sun hada wani abu mai kyau da inganci, gidauniya kan saya, kuma su ne ke fadin kudin da za a saya, mu kan saya a nan take, mu ba su kudinsu, ba tare da neman wani ragi ba, mu na yin haka ne domin mu nuna ma su cewar wannan gidauni, gidauniya ce da ke da bukatar tallafa wa rayuwarsu, tun su na cikin gidauniyar.kuma da zarar mun sayi abin da suka yi, a kwai wajen sayar da kayayyakin da mu ka saya daga wadanda mu ke koya ma su sana’o’in a nan mu kea je wa, wasu mutane suna zuwa dare da rana suna saye a wajenmu.

 

Akwai wasu tallafi da ku ke samu daga gwamnatoci uku, wato kananan hukumomi da jihad a kuma tarayya domin kara bunkasa ayyukan wannan gidauniya?

Babu ko shakka ba mu taba nema ballanta mu samu, kamar yadda na bayyana ma ka wannan gidauniya ta wani bawan Allah ne, babu abin da ba ya yi ma na, domin mu sami damar aiwatar da ayyukan da mu ka sa wa gaba., kuma a shekara shidan da nayyana a baya, duk karshen wata, a kwai kudin da ya ke bayar wa domin gudanar  da ayyukan gidauniyar, sai dai kuma a kwai wani bawan Allah da ya zo wuce wannan gidauniyar, ya yi sallama ya bayar da tallafin Naira dubu hudu, shi a tunaninsa kila gidan marayu ne, mun karba mun kuma yi ma sa godiya sai kuma wata mata da ta kawo ma na Naira dubu goma ta ce, mu sayi Indomin mu dafa wa yaran da ake koya ma su sana’o’I a wannan gidauniya, dukkansu mun yi ma su godiya, ai sun fi ma su tarin kudin da  ba su sun jarinsu, domin samun sakamako a gobe ba.

 

Wani farin ciki ku ke samu daga wadanda kuka koya ma su sana’o’i bayan sun bar wannan gidauniya?

Lallai mu na samu, a kwai wanda ya koyi ilimin kwamfuta, ya sa takardar shaidar da mu ka bas hi, ya sami a aiki a wata babbar ma’aikata da wasu da suka koyi sana’a suna zuwa suna yi ma na godiya da canjin rayuwar da suka samu.

 

A karshe, akwai wani shirin bude reshen gidauniya a wasu wurare musamman ma na yadda ki ka bayyana ma na yadda wasu ke zuwa daga garuruwa ma nisa?

Kamar yadda na bayyana ma ka a baya, wannan gidauniya ta na karkashin wani bawan Allah ne daga jihar Legas, in ya motsa domin bude wani reshe, hakan zai tabbata in Allah ya yadda.e
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: