Daga Mahdi M. Muhammad
Babban bankin Nijeriya (CBN) ya ce ya raba Naira Tiriliyan 1.487 a karkashin shirinsa na habaka noma don bunkasa wadatar abinci.
Gwamnan Babban Bankin, Godwin Emefiele, ya bayyana haka yayin gabatar da sanarwar game da taron Kwamitin manufofin kudi (MPC) wanda aka gudanar a ranakun Litinin da Talata a Abuja.
Emefiele ya ce, bankin koli ya raba naira biliyan 107.60 ga manoma 548,109 da ke noma hekta 703,619 a tsakanin zango na hudu na shekarar 2020 da zangon farko na 2021 don bunkasa noman rani.
Ya ce, “jimillar kudaden zuwa karshen watan Fabrairu na 2021 sun kai tiriliyan N1.487 a karkashin shirye-shiryen noma daban-daban, wanda aka fitar da Naira biliyan 686.59 a karkashin tsarin kirkin Kasuwanci (CACS).
“Bankin ya kuma raba Naira biliyan 601.75 a karkashin shirin na ‘Anchor Borrowers Programm’ (ABP) ga manoma 3,038,649 don tallafawa samar da abinci da kuma rage matsalolin hauhawar farashin kayayyaki. A karkashin ‘Targeted Credit Facility’, bankin ya bayar da Naira biliyan 218.16 ga masu cin gajiyar 475,376, wanda kashi 34 na wadanda suka amfana da shirin SME ne.
“A karkashin tsarin zuba Jari na kasuwancin noma da tamakawa kanana da matsakaitan masana’antu (AGSMEIS), an bayar da Naira biliyan 111.62 ga masu cin gajiyar 28,961, wanda kashi 70 daga ciki suna bangaren noma ne.”
Gwamnan ya ce, bankin na CBN ya kuma samar da jari mai yawa ga cigaban matasa ta hanyar masana’antar kirkire-kirkire, a kokarin bunkasa samar da wutar lantarki gami da kudaden kiwon lafiya.
“A karkashin shirin Injiniyancin kirkirar masana’antu da kirkiro wanda aka fi mayar da hankali ga matasa, an raba Naira biliyan 3.19 ga masu cin gajiyar 341, wanda kashi 53 cikin 100 na masana’antar fim ne. A karkashin shirin ‘National Mass Metering Programme’, an raba Naira biliyan 33.45 ga kamfanoni guda tara domin sayen mitoci 605,852. An bayar da Naira biliyan 89.89 a karkashin Kamfanin Inganta kasuwar wutar Lantarki ta Nijeriya (NEMSF 2) ga kamfanonin rarraba kaya guda 11 don inganta masana’antar samar da wutar lantarki a Nijeriya. A karkashin Naira biliyan 100 na Kula da Kiwan Lafiya, bankin ya bayar da Naira biliyan 94.34, kuma a shirye yake ya fadada wurin zuwa ayyuka 85 a masana’antar hada magunguna. Yana da yawa don fadada layukan magunguna, samo MRI guda shida da sauran kayan aiki da habaka dakunan gwaje-gwaje da sauran ayyukan asibiti,” inji shi.
Emefiele ya ce, bankin koli ya kuma bayar da Naira biliyan 803.36 ga ayyuka 228 a sassan bangarori daban-daban na harkar kawance, hakar ma’adanai, samar da karafa da masana’antun kunshe a karkashin Naira Tiriliyan 1.0.