Kwamandan Birgediya ta 1 ta Sojojin Nijeriya a Zamfara, Birgediya Janar Timothy Opurum, ya ce dakarunsa sun samu nasarar rage ayyukan ‘yan bindiga a jihohin Kebbi da Zamfara.
Ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin taron cin abinci don murnar Sallah da aka shirya wa sojoji da iyalansu a sansanin sojoji da ke Gusau, babban birnin Zamfara.
- Obasanjo Zai Zuba Jarin Dala Miliyan 700 A Kamaru
- ‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga, Sun Ceto Ɗalibai 2 A Nasarawa
A cewarsa, a baya matsalar tsaro a yankin ta kasance mai matuƙar ƙalubale, amma saboda jajircewar dakarun soja da hare-hare da aka kai wa ‘yan bindiga, an samu nasara wajen rage barazanarsu.
“Mun sha wahala a baya, amma yanzu mun samu galaba a kan ‘yan bindigar da suka addabi yankin,” in ji Janar Opurum.
Ya jinjina wa dakarun bisa sadaukarwar da suke yi, kuma ya ce rundunar sojin ƙasa ta tura ƙarin kayan aiki domin tallafa wa sojoji.
Daga ƙarshe, ya buƙaci sojojin da su ƙara ƙwazo domin tabbatar da cikakken tsaro da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma.