Mun Samar Da Daftarin Cigaba Na Shekara 10 Ne Domin Kafa Harsashin Inganta Rayuwar Gombawa –Gwamna Inuwa

ALHAJI MUHAMMAD INUWA YAHAYA Shine gwamnan jihar Gombe, a wani hira  da ya yi da ‘yan jarida ciki har da wakilin LEADERSHIP A YAU, KHALID IDRIS DOYA dangane da wani daftarin kundin cigaba da shekara goma masu zuwa da suka samar wato ‘Gombe State Development Plan 2021-2030, ya bayyana cewar kai tsaye an yi hikima da zurfafa tunani wajen fito da tsare-tsaren da za su kai ga kyautatawa da inganta rayuwar al’ummar Gombe kai tsaye, ya bada tabbacin ganin gwamnatinsa ta dukufa wajen aiwatar da tsare-tsaren da aka samar domin tabbatar da cigaba mai daurewa. Ga hirar:

 

Mun ga jama’a daga sassa daban-daban na ciki da wajen Nijeriya ciki da Majalisar Dinkin Duniya mun ga sun halarci wannan taron na gabatar da daftarin cigaba na shekara 10 masu zuwa ko za ka shaida mana ina kuka dosa da wannan shirin?

Kamar yadda kuka tambaya kallabin jadawali ne da muka yi kundi na tsare-tsaren abubuwan da muke ganin in aka yi su Insha Allahu za su kawo cigaba matuka, domin dukkanin abun da ya shafi rayuwar dan adam da gudanar da Gwamnatin gami kuma da ababen da muka ga sun dace na bukatu wadanda muka jinginasu da ainuhin muradun karni wanda ofishin Majalisar Dinkin Duniya ta zayyana, su ne muka tara a guri daya muka sanya su a kan ginshikai guda biyar wadanda muke ganin da iznin Allah idan muka samu yi aiki tukuru muka samu aiwatarwa da su muka kuma cimma burinmu to Insha Allahu al’ummar jihar Gombe za su samu cin gajiyar ribar Romon mulkin Demokradiyya, kowa daga birni da karkara kowa zai samu rayuwa mai inganci. Sannan kuma za mu cimma manufarmu na fitar da al’umman daga kangin rayuwa da su ma za su shiga fagen da za a dama da su har su samu cin gajiyar falalar da Allah ya huwace mana a wannan zamanin.

 

Ginshikai guda biyar kamar ta wasu fannoni kenan?

Kamar su fannin aiwatar da ayyukan tabbatar da jin dadi da walwalar jama’a masu nagartar da za su kyautata  rayuwar dan adam kai tsaye, aiwatar da manyan raya birane da karkara da suka shafi yin hanyoyi, gina asibitoci, Gadaje, kwalbati-kwalbati da irin su Dam-dam da sauransu, fannin da suka shafi inganta tattalin arziki wadanda su kuma ya shafi kamar aikin gona da irin ayyukan da suka shafi jawo mutane ko kamfanonin zuba jari wadanda za su yi masana’antu manya-manya domin mu samu mu ciyar da jiharmu da al’umman mu gaba, kowannenmu ya kasance a iya abun da Allah ya huwace mana kowa ya samu an dama da shi, shi ma kuma ya tabbatar yayyafi ya sauka a kansa.

 

Mataimakiyar babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ta halarci wannan taron har ma ta yi jawabin da ta nuna yabonta kan irin wannan kundin da har ta nuna sha’awar ganin ana cigaba da hakan, shin akwai wani abu takamaimai da suka maka bayani ko hadin guiwa kan wannan shirin?

Ai daga ainuhin asusun kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin duniya (UNICEF), UNDP da ke kula da cigaban kowani bangare da kuma UNFPA da ke kula da yawan mutane da habakarsu da cigabansu duk sun ba mu hadin kai wajen yin wannan tsarin, kuma a bisa fahimtarsu na cewa lallai jihar Gombe tana yin abun da suka kamata wajen tafiyar da lamura shi ya sa ka ga muna tafiya kafada da kafada da su domin cimma wadannan bukatun namu.

 

Sau tari ba samar da tsare-tsaren ba ne matsalar aiwatarwa ne ke gagara, wani tabbaci za ka bayar na cewa lallai za ku bi matakan da suka dace musamman neman goyon bayan bangaren shari’a wajen ganin an aiwatar da shirye-shirye da ke cikin wannan daftarin?

Dukkanin matakan da suka dace tabbas za mu bi wajen ganin an samu nasarar aiwatar da tsare-tsaren da ke cikin wannan kundin, kama daga gabatar da shi a gaban majalisar Dokokin jihar tun da dai dukkanin batun da muke ga jihar Gombe muke yi kuma wannan daftarin jihar ya shafa kai tsaye, na tabbatar tun da daman ainuhin tun daga farin wannan tsarin mun jawo ‘yan Majalisa cikin kwamitocin da aka yi tun daga tsari har zuwa shiryawa za mu kuma shigar da su cikin cikin lamarin aiwatarwa, don haka na tabbatar za mu samu goyon bayan Majalisar Dokokin jihar Gombe domin su ma wani bangare ne a gwamnatance na tabbatar za mu samu amincewa da goyon bayan Majalisar jihar ta fuskacin maida wannan tsarin domin ya zama doka. Idan lamarin ya huce haka kuma duk kokarin da za mu iya yi za mu yi, muddin muka tabbatar al’umma sun fa’idantu sun aminta sun ga abun da aka yi ko ake sun yi bisa amince da yarda; don za mu yi shi bilhakki da gaske, don na tabbatar kowa zai aminta da tsarin. Idan muka samu amincewa mutum ko iblis ne ya zo ai zai hakura ya bi tsarin da mutane suke so, don haka za mu yi iyaka kokarinmu mu ga cewa an aiwatar kuma mun yi tsarin da kowa daga cikin ma’aikata ya yi abun da ya dace da ‘yan siyasanmu domin a gudu tare a tsira tare, idan aka yi hakan na tabbatar al’ummanmu da suke kasa za su bamu hadin kai da goyon baya yadda wannan tsarin zai zama kamar koda wani ma zai zo sai dai ya kara ba dai ya rage ba.

 

Wani albishir za ka yi wa Gwambawa dangane da wannan kundin?

Kamar yadda suke ganin yadda muke tsayuwa kai da fata wajen yin ayyuka yau kusan a kowani sashi, sako ko lungu ko bangare haka za mu cigaba da yi domin tabbatar da kyautata rayuwar al’umman jihar nan. kuma insha Allah wannan albishir da zan musu dukkanin wannan manufofin da muka zayyana da abubuwan da muka shirya yi za mu tabbatar da taimakon Allah mun cimmasu. Na kuma ba su tabbacin lallai an yi tsari masu kyau da rayuwa za ta kyautata daga kowace bangare na rayuwa. Al’ummar birane da karkara kowa zai amfana matuka daga wannan tsarin. Dukkanin wannan manufofin da ababen da muka shirya yi da izinin Allah za mu cimma nasarori kuma na tabbatar idan aka aiwatar da wannan tsarin kowa ma zai samu dama, kowa zai samu zama cikin lafiya da aminci wanda shine babban abun da ake nema, rayuwar da ta kuma saukaka.

 

Akwai wani shiri da gwamnatinka ta sanya a gaba na samar da wutar kan layuka daga hasken rana me ya sanya Gwamna rungumar wannan shirin?

Dalilai da daman gaske, amma bar na maka bayani. Abun da na zo na tarar an haska wutar kan layi na cikin gari ne ta hanyar daura su a kan Janareto, kuma kwangilar da aka yi kafa sanduna har aka zo ga Janaretoci abun da ake kashewa a tsarin da yake nan a kowani shekara ana kashe miliyan 550 domin a rike wannan tsarin na samar da hasken kan layuka kawai. Kuma ka san illarsa dai a yanzu musamman mu da muka duba cewa dole ne mu inganta muhalli  kuma akwai sabon tsarin da muka yi nazari a kansa wanda in aka samar zai taimaka kuma wuri ba zai gurbata ba, za kuma a samu haske mai inganci, kuma ba shi da tsada idan ka duba alfanunsa ga kuma dadewa. Wannan aikin da za mu yi kilomitoci ne ba mita ba, kilomita har saba’in da kusan biyu zai ci a cikin garin Gombe kusan ko’ina za mu maida shi hakan, sannan kuma mun daidaita da su a kan, a maimakon miliyan dari biyar a kowani shekara misali in ma bai karu ba saboda kudin Mai dai ya karu, kudin Janareta ma ya karu kudin komai ma ya karu. Wannan kuma idan muka rigaya muka yi a yanzu iyaka mun yi daidaito da wannan kamfanin za a shafe shekaru 5 ba mu bada ko kwabo ba, duk abun da ya shafi wannan muna da tabbacin za su gyara har sai mun tabbatar mun biya mukatarmu na amfanuwa, sannan kuma har ila yau yaranmu da suke nan wadanda a kullum muna tunanin a samar musu da gurbin zama da za su yi dan aikin dogaru da kai, za a koya musu sanar yin wannan, in ma ta daure mana nan gaba za mu so masu yin wannan su zo su kafa masana’anta a jihar gaba daya ma. Don haka ni ina ganin za mu samu cigaba sosai da rage kashe kudade ta hanyar samar da wannan layukan wuta masu amfani da hasken rana. Kuma ina ganin wannan tsarin da muka yi a yanzu kusan ba mu da wata tsarin da ya wuce mu rungumi hakan.

 

Gwamnati ta kan samar da kayayyaki ga jama’anta, a maimakon jama’a su tsaya su kula sai su ce ai na gwamnati, wani kira kake da shi ga jama’a da su kula da wadannan kayan hasken idan an samar?

To, ai mu a wannan tsarin kariyarmu na da yawa, mu dai muna da yarjejeniyar cewa wannan kamfanin za su rike wannan na tsawon shekara biyar, dukkanin abun da ya samu turakar hasken wuta babu ruwan gwamnati kamfanin ya shafa, idan jama’a sun ga turakarsu bai kawo wuta ba, su sanar da gwamnati mu kuma za mu kama kamfani su gyara wannan shine ka’idarmu. A gefe guda kuma a kullum ina fada kan cewa a kasa a tsare a raka a jira din nan ba kawai ga kuri’a bane, dukkanin aikin da aka yi ko ababen da aka samar walau makaranta, asibiti wuraren tafiyar da lamura duk abubuwan da aka samar dole ne jama’a su tsaya su kare domin sai ka mutunta kanka kafin wani ya mutunta, ya kamata jama’a suke rungumar dukkanin ababen da aka samar musu hannu biyu biyu domin cin gajiyar kayayyakin.

Exit mobile version