Khalid Idris Doya" />

Mun Samu Nasarar Gudanar Da Sahihin Zaben Gundumomi A Bauchi -Dakta Tony

Shugaban kwamitin gudanar da zaben fidda jagororin jam’iyyar APC a jihar Bauchi Dr Tony Macfoy ya bayyana cewar sun samu gagarumar nasara wajen gudanar da sahihin zaben jagororin jam’iyyar APC a matakan Gundumomi 212 da suke fadin jihar ta Bauchi.

Dakta Macfoy ya bayyana hakan ne da yammacin jiya a sa’ilin da ke shaida wa manema labaru yadda suka gudanar da zaben a jihar Bauchi, ya yi musu bayanin ne a sakatariyar jam’iyyar da ke Bauchi.

Dr. Tony Macfoy ya shaida cewar duk da kasancewar sun fara gudanar da zaben a kurarren lokaci a ranar Asabar, hakan bai hana musu nasarar gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali ba, ya bayyana cewar har zuwa kammala gudanar da aikin basu samu rahoton wata rikici ko tashin hankali ba.

Ta bakinsa, “Zaben da muka jagoranta, zabe ne na cikin gida, mun kuma jagoranci gudanar da wannan aiki bisa yadda dokar da aka bamu na yin zaben muka tafiya a kai. Kowa zai sayi fom domin a tabbatar kai dan takara ne, na biyu kuma idan ma mutum bai samu zarafi a jiharsa an saida masa fom din ba; mu ma muna saida fom din, sannan kuma kada kowa ya mance shi wannan fom din a banki ne, daga nan kuma sai ka amshi fom bayan ka kawo tela,” In ji shi.

Ya ci gaba da bayyana cewar sun yi gagarumar nasara wajen gudanar da zaben nan, “Mun yi zaben nan lafiya mun kuma samu nasarar kammalawa ba tare da wani matsala ba. Mun fara aikin a rana daya, kuma a ranar muka kammala zabenmu lafiya, kamar yadda aka umurcemu mu gudanar a ranar 5/5/2018,” In ji shugaban.

Dakta Macfoy ya kuma karyata zancen tashin hankalin da har yayi sanadiyyar banka wa sakatariyar karamar hukumar Ningi da ke Bauchi kan wannan zaben, inda yake cewa “Ni a bakunku na ke ji, in ban da yanzu da kuke shaida min, ni ban san ma an kona wata sakatariya ba,” A cewar shugaban.

“Kun zo nan sakatariyar jam’iyyar, har kuka zo ba ku ga wani ya cakwami rigar wani ya yaga masa ba; kuma har muka yi zaben nan babu wani da ya ce mana yana da korafi har zuwa yanzu, don haka zabenmu mun yi ne cikin nasara,” In ji shugaban Congress a jihar ta Bauchi

Da yake amsa tambayoyin manema labaru, Sakataren kwamitin, gudanar da zaben Congress a jihar ta Bauchi Alhaji Lawan Abdullahi Kenken ya misanta zancen cewar wasu gungun ‘ya’yan jam’iyyar sun ware domin sake gudanar da wani zabe baya ga wanda suka jagoranta, yana mai bayanin cewar sun yi zabe cikin kwanciyar hankali ba tare kuma da samun wata matsala ba; “Ni dai na sani, cibiyar jam’iyyar a matakin kasa ta turo mu a bisa tsarin da jam’iyyar ta shifida, duk kuma wani da zai zo ya yi wani aiki baya ga namu to ka ga bamu san da shi ba,” In ji Kenken.

Ya kuma bayyana cewar sun gamsu dari bisa dari da yadda zaben ya gudana, ya kuma bayyana cewar dukkanin wani mai korafi kan zaben akwai kwamitin amsar korafi da zai zo domin jin koken kowa, don haka yake bayyana cewar a tasu bangaren babu wani matsala, yana mai cewa su dai sun jagoranci zaben kuma cikin kwanciyar hankali.

 

Exit mobile version