Daga Muhammad A. Abubakar
An bayyana Kungiyar masu fafutikar ganin sun kafa kasar Biyafara wato IPOB a matsayin wadanda ake daukar dawainiyarsu daga gamayyar Barayin Gwamnati da suka saci kudin kasa, da kuma wasu daidaiku masu kokarin ganin sun kawo cikas ga Gwamnatin Buhari da sunan kwato ‘yancin al’ummar Kudu maso Gabas na kasarnan.
Ministan Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Muhammad ne ya bayyana haka a jihar Legas. Ya ce; “ya kamata ‘yan Nijeriya su sani cewa; ba a kirkiri ‘yan Kungiyar IPOB domin ta kwato ‘yancin daidaiku ko gungun mutane ba, illa kawai su wasu makami ne da ake son amfani da su wajen durkusar da kasarnan, tare da kautar da hankulan al’umma daga kokarin da gwamnatin Buhari ke yi na ayyukan ci gaba da bajintar gwamnati ke nunawa.” Ministan ya bayyyanawa ‘yan Jarida a wani taro ranar Lahadi a jihar Legas.
Ya ci gaba da cewa; “’Yan Kungiyar IPOB ana daukar dawainiyyarsu ne daga mutanen da zan kira gamayyar ’yan siyasa masu kokarin kawo cikas wadanda Barayin Gwamnati ne da suka saci arzikin kasa. Sun yadda da cewa; daukar dawainiyyar wannan Kungiya domin su hargitsa kasarnan, zai ba su damar cimma manufarsu na tsallake hukunci da kuma kara samun damar cika hannunsu da arzikin kasa.”
Ministan ya yabawa Sojojin Nijeriyar bisa ayyana ‘yan Kungiyar IPOB da suka yi a matsayin ‘yan Ta’adda da kuma yin bincike kan kungiyar. Sannan ya yabawa Gwamnonin Kudu maso Gabas bisa haramta ayyukan IPOB da suka yi.
Ya ce; “ba don matakin da Sojoji suka dauka ba, da kuma matakin da Gwamnonin Kudu maso Gabas suka dauka na haramta kungiyar ba, da yanzu Kungiyar IPOB sun hargitsa Nijeriya.” Inc ji shi.
Alhaji Lai Muhammad ya zargi ‘yan kungiyar IPOB akan yadda suke kirkirar bidiyoyi cikin jini wanda suka faru a nisan wuri ko wasu kasashe domin su yaudari al’ummar duniya da nuna cewa ana zaluntar mutanen kudu maso Gabas ne a wannan kirkirarrar rigimar kabilanci da kiyayya da wasu ke daukar dawainiyya domin su samu goyon baya da tausayi, inda bayyana wannan mataki a matsayin karya tsagwaronta da kuma farfaganda. “Irin wadannan Bidiyoyi masu taba zukata suna yawo a kafafen sada zumunta, muna kira ga kowa da su saka lura sosai domin ka da a yaudare su. Sannan muna kira ga al’ummar duniya, ka da su yi saurin yanke hukunci, saboda wadannan Bidiyoyi da suke gani.” Sannan Ministan ya roki kafafen watsa labarai, da su sa lura sosai da yin bincike da kuma kaucewa son zuciya wajen kawo rahotannin da suka shafi ayyukan Sojoji wanda suke kaddamarwa wato Operation Python Dance II a Kudu maso Gabas. “ra’ayoyi na raba kan al’umma da wasu masu son kawo hargitsi suke bayyanawa suna samun dama ne daga kafafen watsa labarai. Wannan sam bai dace ba. Bari na tuna muku, gudummawar da kafafen watsa labarai suka bayar musamman Rediyo a shekarar 1994 a lokacin kisan kiyashi a kasar Rwanda wanda ya yi sanadiyyar kashe mutane 800, 000.”
Ya ce; kafafen watsa labaran Nijeriya ba su ga ta zama ba, ko yin ayyukan Jarida wanda ba su dace ba, bayan kuma ana maganar wanzuwar Nijeriya ne.