Mun Shiga Gagarumar Matsalar ‘Yan Wasa -Klopp

Klopp

Daga Abba Ibrahim Wada

Mai horar da kungiyar kwallon kafa Liverpool Jurgen Klopp, ya harzuka matuka da raunin dan wasan tsakiyar kungiyar Fabinho ya yin karawarsu da kungiyar Midtjylland karkashin wasannin cin kofin zakarun Turai da suka fafata a ranar Talatar data wuce.

Fabinho dan Brazil ya bi sahun dan wasan bayan kungiyar Virgil Van Dijk wanda yaji rauni a satin da suka buga 2-2 da Everton da Joel Matip dukkanninsu masu tsaron bayan Liverpool da ke ci gaba da jinya, wanda ke matsayin babban kalubale ga tsaron bayan kungiyar dai-dai lokacin da wasannin sabuwar kaka suka kankama.

A kalaman Jurgen Klopp bayan tashi daga wasan na ranar Talata da Liverpool ta yi nasara da kwallaye biyu da nema, ya ce sam raunin na Fabinho ba shi suka yi fata ba kuma sun shiga gagarumar matsalar ‘yan wasan baya.

Kafin yanzu dai Klopp na amfani da Fabinho ne don cike gurbin Ban Dijk wanda ya samu rauni tun ranar 17 ga watan nan ya yin karawarsu da Everton hakan kuma na  nuna cewa raunin na Fabinho a yanzu zai sanya Klopp a tsaka mai wuya wajen laluben wanda zai cike gurbin ‘yan wasan biyu masu matukar amfani ga tawagar.

Yanzu haka dai matashin dan wasan na Liverpool mai shkearu 19 daya dawo daga aro, Rhys Williams ne zai hada karfi da Joe Gomez wajen rike bayan kungiyar har zuwa lokacin da manyan ‘yan wasan bayan zasu warke su koma fili.

Sai dai ko a bara mai koyarwa Jurgen Klopp ya koka da yadda ake yawan jikkata masa ‘yan wasa ba kuma tare da daukar mataki ba akai daga hukumomi wanda hakan yasa a halin yanzu yayi kira akan a sake saka ido akan yadda ake nunawa ‘yan wasan nasa keta.

 

Exit mobile version