Mun Tafka Asarar Naira Biliyan Biyu – Shugaban Kungiyar ’Yan Goro Na Kano

Daga Mustapha Ibrahim, Kano

 

Alhaji Salisu Auwalu sabon shugaban kungiyar masu sana’ar siyar da Goro na Kano da ke Mariri kasuwar Goro mafi girma a nahiyar Africa ko ma duniya baki daya, ya bayyana cewa sakamakon zuwan Korona Nijeriya wadda ta tilastawa Gwamnatin tarayya da Gwamnatocin jahohi kulle gari na tsawon lokaci wannan ya yi sanadiyyar tafka asara da ta kai kimanin Naira miliyon 800 mu masu wannan sana’a ta cinikin Goro da muke yi a nan kasuwar Mariri da ke cikin karamar hukumar Kumbotso Jahar Kano Nijeriya.

Shugaban kungiyar yan Goron Salisu Auwalu ya bayyana haka ne ga manema labarai, jim kadan da rantsar da shi da sauran masu taimaka masa da aka zaba wanda za su yi shekara uku a wannan mukami a karo na farko a kungiyar kamar yadda tsarin mulkin kungiyar ya tanada a kungiyance.

Har ila yau ya ce baya ga asarar da korona ta haddasa na miliyoyin daruruwan Nairori haka kuma ta faru tun lokacin da Gwanmatin tarayyar Nijeriya ta rufe kan iyakoki sakamakon daukar matakan tsaro da Gwamnatin Nijeriya ta bayyana a wancan lokaci wanda wannan ya kawo wa masu wannan sana’a tafka asara ta kimanin Naira Biliyon Guda sakamakon rufe iyakokin Nijeriya. Saboda haka ya roki Gwamnatin Kano ta Dr. Abdullahi Umar Ganduje kan ta sa su cikin tallafi na musamman domin farfado da jarin da suka rasa sakamakon abubuwa da suka faru na korona da rufe iyakokin kasa.

Haka zalika ya kara da cewa shi Goron ana shigowa ne das hi daga kasashe daban daban kamar kasashen Afrika irin su Ghana, Barkinafaso, Kodubuwa, Kwatano da dai sauran su wanda kuma an samu tashin gwaron Zabbi, inda akan samu buhun Goro Daushe na kai kimanin Naira dubu 250 kuma duk nan ake kawo su kasancewar wannan kasuwar ce mafi girma da aka sani a duniya.

A karshe ya koka da yin korafi ga Gwamnatin Kano da ta karamar hukuma kan neman agajin gina musu magudanen ruwa a kasuwar ta Mariri da sauran matsaloli da suka damu kasuwar da ke bukatar kulawa daga Gwamnati musamman idan aka yi la’akari da yadda kasuwar ke bada gudunmowa wajen samawa dunbun matasa aikin yi da kuma biyan haraji dai dai da tsarin Gwamnati na kowa ya bada gudunmowar sa wajen gina Kano da Nijeriya.

Exit mobile version