Mun Tara Naira Biliyan 140 Domin Samar Da Sinadaran Sarrafa Takin Zamani – FEPSAN

FEPSAN

Daga Abubakar Abba

 

Kungiyar masu sarrafa wa da rabar da takin zamani ta kasa (FEPSAN) ta shelanta cewa, ta tara sama da Naira biliyan 140 na gundarin kudi domin sarrafa takin zamani a kakar bana.

 

Babban Sakataren kungiyar Mista Gideon Negedu ne ya sanar da hakan a ranar Litinin da ta gabata a  babban birnin tarayar Abuja ba wani taro na cibiyoyin samar da kudade da kuma dilolin sayar da takin zamani.

“Mun tara kimanin Naira biliyan 140 domin samar da sanadaran da ake saffara takin zamani za mu kuma kara samar da wani tallafin domin samun saye da dama”.

 

A cewar Mista Gideon Negedu, kungiyar na ci gaba da fuskantar kalubale kan yadda ake samun gurbataccen talkin zamani, inda ya kara da cewa, wannan shi ne babban kalubalen da masana’atun sarrafa takin zamani a kasar nan ke fuskanta, musamman wajen samo masu son zuba jarinsu a fannin.

 

Ya yi nuni da cewa, idan ka bukaci manoma su zuba jarinsu a fannin sarrafa takin zamani, ma’ana kana sa masu yarda ce a zukatansu, musaman domin su samu riba mai dimbin yawa da kuma samun amfanin gona mai yawa.

 

“Manoma na sayen gurbataccen takin zamani ba tare da sun sani ba, inda ya kara da cewa,a a saboda hakan ne, muke bai wa manoma shawarar su yi amfani da takin zamani na FEPSAN ganin cewa, ya na inganci.”

 

“Kungiyar na ci gaba da fuskantar kalubale kan yadda ake samun gurbataccen talkin zamani, inda ya kara da cewa, wannan shi ne babban kalubalen da masana’atun sarrafa takin zamani a kasar nan ke fuskanta, musamman wajen samo masu son zuba jarinsu a fannin,” in ji shi.

Negedu ya yi kira ga gwamnati da ta samar da tsaro ga manoman da ke a kasar nan domin su samu sukunin zuwa gonakansu yin noma.

A jawabinsa, Darakan shirin aikin noma na Afirka  (AGRA) Dakta  Kehinde Makinde, wanda Mataimaki  a AGRA Ndem Chijioke ya wakilce shi a gurin taron ya sanar da cewa, a 2018 AGRA ta samar da tallafin takin zamani ga masu sarrafa takin da sauransu.

 

“A ne 2018 aka fara gudanar da aikin kuma an tanadar da kyakyawan tsari ga kananan manoma kuma za a gudanar da bita ga masu sarrafa takin da kuma dilolinsu.”

 

Exit mobile version