Mun Tsame ‘Yan Nijeriya Miliyan 10.5 Daga Kangin Talauci A Cikin Shekara Biyu – Buhari

Daga Sulaiman Ibrahim

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta fitar da mutane miliyan 10.5 daga kangin talauci a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Ya bayyana hakan ne a safiyar yau a jawabin da ya gabatar na Ranar Dimokaradiyya ta bana.

Shugaban ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa burin da ake da shi na tsamo ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga kangin talauci za a iya cimmasa.

Ya ce; “A cikin shekaru biyu da suka gabata, mun fitar da mutane miliyan 10.5 daga kangin talauci – manoma, kananan ‘yan kasuwa, masu sana’o’i, mata ‘yan kasuwa da makamantansu.

“Ina da matukar yakinin cewa za a iya cimma wannan buri na miliyan 100 kuma wannan ya bayyana nasarar cigaba da rage talauci da kuma samun dabaru na cigaban kasa.

Shugaban ya kuma sake nanata kudurinsa na samar da yanayi na ba da ‘yanci, gaskiya da amintaccen tsarin zabe a karkashin mulkinsa.

Exit mobile version