Mun Yaba Da Kokarin Kamfanin Bizi Mobile – Gwamnatin Kano

Daga Ibrahim Ibrahim, Kaduna

A yunkurinsa na ganin a ko da yaushe yana kawo ma Yankin Arewa abubuwan ci gaba irin na fasahar zamani, domin inganta rayuwar Mata da Matasanmu.

Kamfanin hada hadar kudi da fasahar kimiya irin ta zamani, wato Bizi Mobile Cashless Consultant limited, ya shirya ma daukacin Matan Jihar Kano, taron wuni biyu, ta hanyar basu ilimin yadda zasu yi kasuwancin siye da siyawarwa a sauwake. Taron wanda a turance akayi ma lakabi da “E-commerce, Agency Banking and An Edhibition”.

Akalla sama da Mata 200 ne daga kowane sassan kananan hukumomin 44 dake Jihar Kano, Kamfanin Bizi Mobile ya horar dasu dabarun kasuwancin siye da sayarwa irin na zamani a sawwake.

Taron wanda ya gudana a dakin taro na Tourism camp dake cikin Garin Kano, ya sami halartar manyan Jami’an Gwamnatin Jihar Kano, Sarakunan Gargajiya, wakilan bankuna, kamfanoni, da Shugaban kamfanin Peper Soff, Mista Tony Eze, wanda yazo daga Jihar Lagos, da kuma sauran manyan baki.

A yayin da yake jawabi, Shugaban kamfanin Bizi Mobile, Alhaji Dakta Aminu Aminu Bizi, ya bayyana makasudin shirya wannan taron bita domin wayar da kan Matan Jihar Kano na wuni biyu. A inda ya bayyana cewa, “makasudin shirya wannan taron bita na wuni biyu da kamfaninmu ya yi, shi ne domin mu koyar da Matanmu yadda zasu yi kasuwancinsu daga gida ba tare sun sha wata wahala ba. Domin yanzu zamani yazo mana da abubuwa masu yawa, musamman a harkar kasuwanci irin na sadarwar zamani wanda a turance ake kira da E-commerce.”

High Chief Aminu Bizi ya kara da bayyana cewa, “mun yarda da cewa Allah shi ke da zamani, kuma duk abin da zamani yazo da shi dole mu rungumeshi, saboda ko babu komai akwai ci gaba da ilimi a harkar kasuwancin zamani.”

“Matanmu na Arewa na da dimbin hazaka da basira wajen iya naiman na kansu, amma babban matsalarsu itace, marketing”ma’ana yadda zasu tallata hajarsu”. Wannan dalilin ne ya sanya mu tunanin mu tarasu domin mu koyar da su yadda ake siya da siyawarwa irin na zamani. Babban abin da zai baku mamaki shi ne, daga cikin Matan nan akwai wacce da kanta take hada takalma, akwai masu hada manshafawa da sabulai masu kyau da kamshi, akwai wacce take hada jaka da gyale, akwai masu hada huluna irin na Mata, da dai sauran su.”

Dakta Aminu Aminu Bizi ya kara da bayyana cewa, “Babban abin da muka lura shi ne, gasu da haja ta siyarwa amma basu san inda zasu kai ba, sai dai wanda suka tallata mawa a gida ya siya, amma basu da hanyar da zasu iya tallata shi duniya ta gani. Shiyasa mukayi amfani da wannan dama muka koyar da su hanyar da zasu bi domin siya da kuma siyar da hajarsu a sawwake, suna zaune a cikin gidajensu batare da sun je ko ina ba.”

Shima a nasa jawabin, Wakilin Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wanda Kwamishinan Kasuwanci da zuba jari na Jihar Kano, Barista Ibrahim Muhammad Umar, ya wakilta, a madadin Gwamnatin Jihar Kano, ya Jinjinawa kamfanin Bizi Mobile karkashin jagorancin Shugaban kamfanin Dakta Aminu Bizi, a bisa Namijin kokarinsa na wajen ganin a ko da yaushe yana kawo ma Al’ummar Jihar Kano abubuwan ci gaba.

Gwamnan Jihar Kano ya kuma kara da bayyana cewa, a shirye suke da su ci gaba da hada hannu da kamfanin Bizi Mobile domin ganin sun samarwa Matasa da Al’ummar Jihar Kano ayyukan yi, musamman akan abin da ya shafi hada hadar kasuwanci irin na zamani, domin a cewarsa, hakan zai samar da dimbin ayyukan yi ga Matasan Jihar Kano, da kuma kara bunkasar tattalin arzikin jihar baki daya. Sannan ya taya murna ga daukacin Matan Jihar Kano da suka sami nasarar samun wannan tallafi ilimin kasuwanci kyauta da kamfanin Bizi Mobile ya basu, sannan ya horesu da mai da hankali akan abin da suka kowa domin ganin sun yi aiki da shi.

Da yake sanya albarka a matsayinsa na Babban bako a wajen taron, Sarkin Shanun Kano, Dakta Shehu Muhammed dankade, ya yaba ma kamfanin Bizi Mobile matukar gaske, saboda wannan gagarumin gudunmuwa da kamfanin ya baiwa Matan Jihar Kano, wanda a cewarsa, yin hakan ba karamin ci gaba da alfanu lamarin zai haifar ba.

Itama a nata jawabin, Kwamishiniyar ci gaban harkokin Mata da walwala ta Jihar Kano, Dakta Zahra’u Muhammad Umar, wacce ta sami wakilcin Babban Darakta a ma’aikatar, Hajiya Bilkisu Shafi’u Jibril, ta roki ‘Yan uwanta Mata da cewa, yanzu lokacin zaman kishi ya wuce a tsakaninsu, a cewarta yanzu lokaci ne da zasu tashi tsaye domin naiman na kansu da kansu har su tallafawa na kasa da su.

Kwamishinan ta kuma Jinjinawa kamfanin Bizi Mobile, a bisa wannan gudunmuwar da kamfanin ya kawo ma Al’ummar Jihar Kano, musamman tallafin da ya kawo ma ‘Yan uwanta Mata. Ta kuma bayyana cewa, kofar ta a bude yake domin hada hannu da kamfanin Bizi Mobile domin inganta rayuwar Matan da Matasan Jihar Kano.

A yayin taron bitar na yini biyu, kamfanin Bizi Mobile ya bayar da kyautar lambar yabo ga wasu daga cikin shahuran mutane da suka bayar da muhimmiyar gudunmuwa a rayuwarsu, wanda suka hada da; Kwamishinan Kasuwanci da zuba jari na Jihar Kano, Barrister Ibrahim Umar, da Kwamishiniyar Mata ta Jihar Kano, Dakta Zahra’u Muhammad Umar, da Sarkin Shanun Kano Dakta Shehu Muhammed dankade, da Matawallen Kazaure, Bashir Adamu Jumbo, sai kuma Wakilin jaridar Leadership A Yau, Ibrahim Ibrahim, da Nasiru Salisu Zango.

Exit mobile version