Connect with us

RAHOTANNI

Mun Yaba Da Rabon Kayan Tallafi A karamar Hukumar Nassarawa – Sani Sale

Published

on

An yaba da yadda a ke rabon kayan tallafi a karamar hukumar Nassarawa da ke Jihar Kano a cigaba da rage radadin halin da al’umma su ka shiga na annobar cutar Korana da ta addabi fadin duniya da Nijeriya, wannan ne ya sa Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin taimaka wa jihohi da kayan tallafin abin masarufi, domin marasa galihu. Wannnan ya sa Gwamnatin Jihar Kano karkashin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta bada umarnin raba wa kanannan hukumomin jihar ta karkashin sarakunan gargajiya.

Idan ba a manta ba, da ma gwamnatin jihar tuni ta kaddamar da ciyar da mutane 300,000 a fadin jihar kafin Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin taimaka wa jihohi. karamar Hukumar Nasarawa da ke cikin birnin Kano ta samu irin wancan kayan na Gwamnatin Tarayya.
Wakilin Gwamnan Jihar Kano kuma shugaban kungiyar masu masana’antu na jihar, Alhaji Sani Husaini Sale, ya samu shaida wa wakiln LEADERSHIP A YAU irin nasarar da su ka samu wajen rabon kayan. Ya ce, wannan shi ne rabo karo na biyu da a ka yi da gwamnatin jihar da na Gwamnatin Tarayya, kuma abinda ya ce, gaskiya wannan wakilan da a ke bai wa wannan kayan kamar hakimai da dagatai da masu unguwanni sun yi abin yabawa, domin tunda a ka fara ba a samu matsala ba wannan dole a yaba mu su.
Ya ce, “kuma da ma wannan kayan kafin ya karaso inda za a raba ansan wanda za a bai wa kowa da sunansa, kuma wakilai wanda su ne dagatai na kowacce mazaba su za su karbi wannan kayan.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: