Abba Ibrahim Wada" />

Mun Yi Asarar Babbar Dama —Emery

BASEL, SWITZERLAND - MAY 18: Unai Emery manager of Sevilla leaves the pitch at the half time during the UEFA Europa League Final match between Liverpool and Sevilla at St. Jakob-Park on May 18, 2016 in Basel, Switzerland. (Photo by David Ramos/Getty Images)

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Unai Emery, ya bayyana rashin jin dadinsa bisa rashin nasarar da kungiyarsa tayi a wasan da kungiyar Crystal Palace taje har gida ta lallasa su daci 3-2 a wasan firimiya.
Dan wasa Cristian Benteke da Wilfred Zaha da kuma Mc Arthur ne suka jefa kwallaye ukun a ragar Arsenal wanda hakan yasa har yanzu kungiyar bata tabbacin zuwa kofin zakarun turai na shekara mai zuwa.
Daga bangaren Arsenal kuma dan wasa Mesut Ozil da Aubameyang ne suka ci musu kwallayensu guda biyu a wasan sai dai wasan baiyi wa kociyan na Arsenal, Unai Emery dadi ba inda yace sunyi asarar babbar dama ta zuwa kofin zakarun turai.
“Munyi asarar babbar dama ta zuwa kofin zakarun turai a shekara mai zuwa sai dai ba wannan ne karo na farko ba da muke yin irin wannan rashin nasarar amma kuma yakamata mu sake dagewa domin ganin mun cimma burinmu” in ji Emery
Yaci gaba da cewa “yaci gaba da cewa haka daman gasar firimiya take kowacce kungiyar zata iya yin rashin nasara a gida amma kuma abinda yakamata muyi shine mu shirya wa wasan da zamu kai ziyara kungiyar kwallon kafa ta Wolbes a ranar Lataba saboda babban wasa ne wanda yake bukatar mu samu nasara”
Arsenal dai tana mataki na hudu da maki 66 yayinda Chelsea wadda take binta a baya a matsayi na biyar itama da maki 66 sai kuma Manchester United a matsayi na shida da maki 64 kuma zata fafata da Manchester City a kwantan wasansu na gobe Laraba.

Exit mobile version