Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Cristiano Ronaldo, ya bayyana cewa kungiyar ta Juventus tayi babban kuskure na rashin nasarar da sukayi a wasan da suka buga da kungiyar kwallon kafa ta FC Porto a gasar cin kofin zakarun turai na bana.
FC Porto ta yi waje da Juventus a gasar Champions League, duk da rashin nasara da ta yi da ci 3-2 a Italiya a wasan da suka yi ranar Talata kuma kungiyoyin sun buga wasa na biyu a gasar cin kofin zakarun Turai don fayyace wadda za ta kai fafatawar wasan kusa dana kusa dana karshe.
Kungiyar ta Portugal ta ci wasan farko da suka yi a cikin watan Fabrairu da ci 2-1, ya yin da Juventus ta ci 3-2, jumulla Porto ta kai zagayen gaba ne, bayan da ta ci kwallo biyu a kasar ta Italiya.
“Bayan tashin daga fafatawar ne dan wasa Ronaldo ya bayyana cewa tabbas dashi da abokan wasansa sunyi babban kuskure a wasan da suka buga kuma hakan ya zama kamar darasi a tattare dasu”
Porto ta karasa fafatawar da ‘yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Mehdi Taremi jan kati a minti na bakwai da komawa zagaye na biyu sannan wannan ne karon farko da Porto ta kai wannan mataki a Champions League, bayan da ta ci wasan farko, tun bayan shekara ta 2003 zuwa 2004 da ta yi nasara a kan Lyon.
A karo na biyar kenan ana cire Juventus a wasan zuwa daf da na kusa da na karshe a Champions League idan aka doke ta fafatawar farko wanda Juventus ta yi bajinta a biyar din shi ne karawa da Atletico Madrid, inda tasha kashi da ci 2-0 a Spaniya, ya yin da ta kai kuarter finals a Italiya, bayan da ta ci 3-0 a kakar wasa ta 2018 zuwa 2019.