Mun Yi Da Na Sanin Zuwa Kasar Libiya –‘Yan Nijeriya Da Aka Dawo Da Su

Migrants from Mali wait at Misrata airport before their return to their countries, in Misrata, Libya September 20, 2018. Picture taken September 20, 2018. REUTERS/Ayman al-Sahili

Kimanin matasa mutum 2,000 ‘yan asalin Nijeriya da aka dawo dasu daga kasar Libiya, sunyi da na sanin zuwan su kasar ta Libiya, matasan sun yi wannan da na sanin ne a daidai lokacin da aka kammala shirin koyar da su sana’o’in dogaro da kai a Ijebu-Ode yau Talata, inda suka bayyana cewa sun gwammace da sun tsaya a kasar su.

A makon da ya gabata ne hukumar kula da ‘yan gudun hijira, da bakin haure ta kasa (NCRMI) ta fara gabatar da wani shirin koyawa mutanen da aka dawo da su daga kasar Libiya sana’o’i don dogaro da kai, tsarin na kwanaki biyar ne, inda za a koyawa duk wadanda aka dawo dasu daga kasar Libiyan sana’a da dogaro da kai.

Wasu daga cikin wadanda suka samu damar samun horon sun shaidawa manema labarai cewa, sun koyi gyaran wayoyin hannu, sannan wasu daga cikinsu kuma sun koyi yadda ake hada sabulu, inda suka ce sun yi matukar yin da na sanin tafiyar su kasar Libiya da suka yi.

Sun bayyana irin yadda suka fuskanci wahalhalu da cin zarafi a yayin da suke kasar Libiya din, inda kasar Libiyan ta zame musu kamar jahannama, sun bayyana cewa yanayin tattalin arzikin da Nijeriya take ciki ne ya sanya suka fice daga kasar don zuwa kasar Libiya neman halaliya, amma sai suka tsinci kansu cikin mawuyacin hali a kasar Libiyan.

Hukumar ta bayyana cewa tana sa ran nan gaba babu dan Nijeriyan da zai yi sha’awar zuwa wata kasar waje, musamman ma kasar Libiya, inda ta shahara da labarai na cin zarafi da azabtarwa, sannan wadanda aka dawo da su din zasu zame ma duk wani mai sha’awar irin wannan tafiyar izina.

Exit mobile version