Ibrahim Muhammad" />

Mun Yi Farin Ciki Da Samun Nasarar Gwamna Ganduje—Bilya Asasco

Shugaban CRC na karamar hukumar Ungogo Alhaji Bilya Asasco ya bayyana matukar farin cikinsa da nasararda Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya samu a kotun sauraren kararralin zabe.

Yace  su sukafi kowa farin ciki a matsyinsu na masoya magoya baya suna godiya ga Allah mai komai mai yanda yaso alokacinda yaso ya basu mulki alokacinda yaso ya kuma kara musu a zango na Biyu.

Alhaji Bilya Asascp yace wannan nasara da Gwamnan ya samu ta samune sakamakon kyakkyawar zuciya da niyya da yake dasu domin kullum Allah yana duban zuciyar dan’adamne  ya taimaka masa  kan abinda yasa a gaba.

Ya kara da cewa kowa ya gamsu Gwamna Ganduje dabi’unsa da halayensa da tarbiyya da yake dashi ta mutuntakace.Suna fata Allah ya tayashi riko domin wannan alkaliya da tayi sharia tayi gaskiya anyi komai a bude kowa ya gani hatta suma masu kara suna tabbatarwa da duniya  tayi abinda yakamata na adalci sun yaba mata.

Alhaji Bilya Asasco yace dama su sukaci zabe akazo da abinda bashi bane  Allah ya tabbatarda gaskiya an baiwa masu gaskiya gaskiyarsu.

Asasco yayi kira da a cigaba da baiwa Gwamna Ganduje hadin kai dayi masa addu’a na alkhairi da fatan yayi mulki ya gama zangonsa na biyu lafiya.Allah ya bashi ikon sauke nauyi da aka dora masa ta irin dinbin ayyuka na cigaban al’umma da yake.

Exit mobile version