SANATA BALA MUHAMMAD ABDULKADIR shine gwamnan jihar Bauchi, a wani hira da ya yi da ‘yan jarida ciki har da Wakilin LEADERSHIP A YAU, KHALID IDRIS DOYA, dangane da wani sabon shirin sarrafa Shara da Datti domin yin amfani da su ta hanyar Makamashi domin samar da hasken wutar lantarki mai girma a fadin jihar, ya nuna cewa irin wannan shirin shine na farko a duk fadin Afrika ba ga kasar Ethiopia. Ya nuna cewa tabbas za a samu dimbin riba da samar wa matasa ayyukan yi ta wannan shirin da kuma kyautata sashin samar wa jihar kudaden shiga. Ga yadda hirar take:
Ga wani shiri da aka kawo jiharka na samar da Makamashi ta hanyar amfani da shara da datti ko kayan da aka watsar, ko za ka mana karin haske kan wannan lamarin?
Mu na godiya wa Allah (S) da ya kawo mu wannan lokacin kuma a wannan sabowar shekara ta 2021 wanda an ce Juma’ar da za ta yi kyau daga Labaranta ake gani. Ga shi na dawo daga tafiya kuma ma’aikatana sun yi aiki tukuru wajen kawo wannan gagarumin Jari da ya zo daga kasar Turai na Ingila wanda za su kawo babban na’ura wanda za su ringa kona datti na cikin garin Bauchi da kewaye ba sai ana dauka ana zubawa a bakin titi ko a gonaki ba.
Wanda zai kasance da shi za a yi amfani ya zamanto dukiya, ma’ana za a maida kayan rashin amfani zuwa ga amfani da shi da zai amfanar da al’umma; za a yi Taki da shi za a yi Makamashi da shi wanda zai sanya wutan lantarki, hakan zai bada dama a samu wuta a garin nan ba tare da ana samun wani matsala ba, kuma kamfanonin da suke garin nan su ma za su sayi wannan wutan kai tsaye idan muka yi magana da gwamnatin tarayya.
Na san za mu hada kai da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari mu taimaka masa mu kuma taimaka wa kanmu mu ga kudurin da yake da shi a kan Makamashi ya yi amfani matuka. A gaskiya wannan aikin abu ne mai kyau da zai kawo cigaba sosai. Su za su kawo dala miliyan saba’in domin su kafa wannan na’ura wanda shi ne irinsa na farko a duk nahiyar Afrika bayan na Ethiopia kuma na yi kokari na so yin irin wannan a birnin tarayya Abuja hakan bai yiyu ba saboda karancin lokaci, amma wannan an fara da wuri insha Allahu kuma tunin mun ba su wurin da muke zuba datti, muna da dattin da ya kai ninkin abun da suke nema, da alama abun da suke nema na lasisi da sauran abubuwan da suke nema duk za a iya musu a cikin wata daya, kuma za a gama komai a fara a cikin watan uku wanda a cikin watanni goma sha biyu za gama komai da komai Insha Allahu mutanen Bauchi za su fara moran wannan sabon tsarin da aka kawo daga kasar Turai na sarrafa datti da shara domin amfani da su ta hanyar Makamashi da Taki.
Yanzu idan mutane suka ji kuna amfani da dattin da suka samar, su sanya a ransu cewa nan gaba za su fara saida datti kenan?
Da ana fada wa jama’a cewa sai sun kwashe datti, to yanzu kuma sai ga shi nan dattin ma ya zama abun kudi, watakila nan gaba dattin ma saya za a ke yi kamar yadda ka fada, haka yake faruwa a wasu kasashen duniya inda a maimakon a baka wahala in ka bar datti daga wajen jami’an duba gari sai ya kasance dattinka ma ya zama abun da za ka iya sayarwa ne; amma mu ba mu kai wannan matakin ba, muna kuma fatan cewa da yardar Allah za mu kai.
Ta wasu hanyoyi gwamnatin jiha za ta mori wannan shirin ta fuskacin samar da aikin yi da kuma bunkasa tattalin arziki?
A wannan kamfanin kawai ita kadai za a dauki Injiniyoyi da matasa dari biyu, su kuma kamfanonin da muke da su, a ‘Industrial Area’ da muke son mu kafa tare da hadin guiwan gwamnatin tarayya da sauran wadanda suke zuwa ana kiyasin cewa za a samu yara matasa sama da dubu biyu 2,000 da za a daukesu aiki a wadannan kamfanonin wadanda za su ke samun wuta mai sauki kuma suke samun riba, jihar Bauchi kuma za ta samu karin kudaden shiga don da kudaden shiga muke wadannan ayyukan hanyoyi da ake gani ba bashi muke dauka ba yadda ake karerayi musamman ‘yan adawa. Mu bashin da ‘yan adawan su ka ci ma muke biya, biliyan 92 na gada na bashin da ake bi; amma ni ban dauki bashi ba, da kudin shiga nake amfani da shi. Ta irin wadannan hanyoyin ne za mu samu kudaden shiga, domin idan mutum na da dama ne zai iya biyan haraji, in kana da kamfani ne za ka iya biyan haraji, don haka a takaice wannan aikin da za a samar zai bada dama a samu bunkasar tattalin arziki, mutane su samu aikin yi kuma a samu ingantuwar ababen more rayuwa.