A ci gaba da bikin bajakoli karo na arba’in da daya wannan cibiyar ta kasuwanci ta ware wasu ranaku domin bawa kamfaninnika gabatar da jawabi a wannan kasuwa domin bayyana duk manufar wannan kamfani ko hukumar gudanarwar da take karkashin gwamnati ko daidaiku.
Wannan ya sa makon da ya gabata bankin masana’antu dake jihar Kano ya yi nasa taron a kasuwar bajakoli da ke jihar Kano Hassan Yaro shi ne shugaban wannan kwamatin na shiryawa duk kamfanoni irin wannan ranaku a kowacce rana a wannan kasuwa.
Kammala wannan taro na bankin masana’antu ke da wuya Wakilinmu ya sami ganawa da shi domin jin ta bakinsa dangane da muhimmancin samar da irin wannan ranaku a cikin wannan kasuwa.
Ya bayyana cewa muna shirya wannan ranaku ne saboda mutane wanda basu da shi ma’ana masu karancin gata. Domin ta wannan hanyar ne wasu zasu samu ba shi ko a siya musu kayan da za suyi sana’a kuma wannan ya hada da masu kananan masana‘antu ko masu manyan masana’antu ma kuma dole za a dunga shan wahala wajan samu domin abu dari gwamnati zata bayar amma za ka ga sama da mutum dubu ne za su je dole akwai wahala kwarai da gaske amma a daure abin da ya kamata asa niyya sosai kaga ai bamu ne masu bayarwa ba, ba zamu ce mutum dari sun nema mutum dari zasu samu ba. A’a za a samu amma a kalla mutum saba’in da biyar zasu samu kuma wannan shi ne taron mu na farko a wannan kasuwa ta bajakoli kuma ganin yanayi da aka shiga sakamakon Korona ya sa komai sai a hankali domin banda nan Abuja na yi, Legos na yi, domin jihohi da yawa sun koke bajakoli.
Shi ma manajan da ya shigo wannan kasuwa ta bajakoli kuma shine manajan bankin masana’antu ya bayyana suna maraba da duk wani mai sana’a, domin bankin ne da zai taimakawa duk wani dan kasar nan, domin ya taimaki sana’ar da ya ke yi domin ya taimaki kasa da sana’ar da ya ke yi ya ce kiran da zai yi shi ne ya yi kokari ya maida duk bashin da aka ba shi, domin wani ma ya je ya karba.