Bello Hamza">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home DAGA TEBURIN EDITA

Mun Yi Shiri Na Musamman Don Ceto Asibitin Koyarwa Na Jami’ar ABU Daga Durkushewa —Farfesa Ummdagas Ahmed

by Bello Hamza
October 6, 2019
in DAGA TEBURIN EDITA
7 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) dake zariya na daya daga cikin manyan cibiyoyin kiyon lafiya da ake tunkaho dasu a yankin arewacin Nijeriya, amma a ‘yan shekarun nan al’amurran asibitin ya tabarbare ta yadda al’umma suka fara guje wa asibitin saaboda rashin samun biyan bukata, akan haka ta kai mai martaba Sarkin zazzau Alhaji Shehu Idris ya koka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da neman dauki ga halin da asibitin yake ciki. Editanmu Bello Hamza ya tattauna da sabon shugaban asibitin, Farfesa Ahmed Ummdagas Hamidu, wanda kwararen likitan kwakwalwa ne, ya kuma rike mukamai da dama a cikin kasar nan, ya yi bayani cikakke a kan halin da ya samu asibitin a lokacin da ya kama aiki a ranar 23 ga watan Mayu na sherkarar 2019, da kuma matakan gaggauwa da ya fara dauka domin dawo da martabar asibitin da kuma irin shiri na musamman da ya yi don ganin dukkan shirye-shiryen da ya yi sun samu dorewa, ga dai yadda hirar ta kasance.

Asibitin nan ya na daya daga cikin manya kuma kwararrun asibiti na farko a Arewacin kasar nan, a wanne hali ka samu asibitin da ka kama aiki?

Dana zo dai a gaskiya akwai matsaloli da dama dana samu a kasa, a takaice a ranar da na fara zuwa ofis dana je bangaren dakin bayar da agajin gaggawa (Emergency unit) musamman rashin tsaro a bangaren don kuma a ranar dana fara ziyartar sashin an sace babur, haka washe gari, dana sake dawo wa aka daukewa wani babur sai na lura lallai akwai matsalar rashin tsaro.

Sai kuma na lura akwai matsala ta rashin tsafta domin datti ya cika ko ina sai na zauma da manyan ma’aikata na dauki matakai na magance wasu matsalolin tunda ba kudi a Asibitin, don kudin da gwamnati take bayarwa basu da yawa. Kuma na’urorin dake aiki a Asibitin duk wasu sun lalace wasu kuma sun tsufa. Toh, ganin hakan, sai nace bari in dauki fannin tsaftar da tsaro a matsayi na gaggawa wato in basu mahimmanci sosai a Asibitin. A cikin watanni uku dana zo, Alhamdulillahi, don tunda dai nazo, maganar rashin tsaro idan kana shigowa zaka ga banbancin inda mutane suke ajiye babura daban ne, ada babu wannan yanzu Allah ya taimakemu babu satar babur. Maganar tsafta kuwa, itama an samu ci gaba sosai a Asibutin don ada in kazo ko ina wari yake yi, na zauna da wadanda suka kamata a kan hakan muka fahimci juna kuma in sha Allahu, zamuci gaba da yin kari a kan hakan.

Dakin bayar da taimakon gaggawa kuwa (Emergency unit), shima a yanzu baya yin wani wari a cikin dan wannan lokacin mun samu mun gyra mun sayi kayan aiki kuma akwai injin bayar da wuta, (janarata) da wani dan karami ne amma mun samar da dan babba wanda in dan dauke wutar lantarki zai iya daukar fanka da kuma dukkan kayan aikin dake dakin, mun gyra makewayi.

Bayan wannan, akwai maganar samar da iskar Odygen don tallafa wa majinyata masu bukatar iska don munfashi, a lokacin da nazo wajen sarrafa iskar (Odygen) na Asibitin baya yin aiki kwata-kwata, dana zo muka matsa aka gyra, yanzu idan kaje cikin Asibitin ko ina akwai iskar ta Odygen ba sai kaje wani waje nema ba, a ciki nan muke sarrafa iskar ta Odygen an samar da kaya masu aiki sosai wanda a takaice, bama shan kashi 50 a cikin dari na abin da muke sarrafawa, saboda haka, nan bada jimawa ba, zamu fara sayar da iskar Odygen ga wasu asiboci don amfani ga masu jinya a awajensu. Wadannan sune ‘yan ayyukan da mu kayi, mu na godiya ga Allah. Sai dai kuma, kamar yadda ka sani, a harkar gwamnati ana yin abinda ake kira ne (Line budget), kasafin kudi kuma kudin da za’a baku bashi da wani yawa, sai ace kudin za’a baku kawai kuma dole ne kayi amfani dasu, ba wani kudi da zaka sake samu, tunda dai na hau, ba wani sabon kudi da aka bani saboda kudin da aka bamu, abinda muke dashi ne muke ta juyawa muke kuma yin wannan ayyukan, Alhamdulillahi. Shi Mai Martaba Sarkin Zazzau Dakta Shehu Idris, ya yi kira a madadin mu saboda ya san halin da muke ciki kuma gwamnati tana yin iya kokarinta don a fita daga matsalolin, amma dai, zuwa yanzu, babu wasu kudi da suka shigo Asibitin nan da sunan wani dauki.

Kafin zuwanka, majinyata sai sun tafi wasu wurare don yin hoton kwakwalwa da sauran gwaje gwaje, wanne hali ake ciki a yanzu?

Yanzu nun kulla yarjejeniya da wani kamfani wanda nan da zuwa kamar wata daya za a samu mafita, sabin na’aurar da muke shirin kafawa na zamani ne wanda zai rinka aiki da intanet, a halin yanzu an kusan kammala ayyukan kafa wayoyin da na’urar za ta yi amfani dasu, in kamala koni da nake a cikin ofis a nan, zan iya ganin hotunan in kuma bayar da rahoto a kai nan take. Injin din kawai muke jira a yanzu, yana da bangare hudu ne, wanda muke dashi da ada ya mutu yana da bangare biyu ne kaga akwai banbanci sosai, majinyata za su daina zuwa ko ina don yin hoton kwakwalwa za kuma a samu sauki kwarai da gaske.

Kana nufin har yanzu babu wani dauki na musamman da kuka samu da wanu bangaori na gwamnati?

Gaskiya dai har yanzu bamu samu wani tallafi ba, mun dai rubuta takardu ga gwamnati muna kuma fatan za su bamu dauki domin idan babu wannan taimakon, akwai matsala, maganar ita ce, Asibitin an gina shi ne tun a shekarar 1972 amma ba’a shiga ba sai a 2005, toh, kaga akwai lalacewar da Asibitin ya yi da yawa don wannan ne kashi na farko na Asibitin, ba’a gama shi ba aka sa muka shiga. A shekaru biyar da suka shige hanyar magudanar ruwan Asibitin wari ne yake fita da inka shigo Asibitin, abinda ke faruwa shi ne, Asibitin yana yana zaune a kan hanyar magudanar ruwa ne, aka haka na samu Darakta Janar na Hukumar bayar da agaji gaggawa NEMA a kan wannan lamarin domin hakan zai iya zama annoba kuma banda ita magudanar ruwan, akwai wayar wutar lantarki a saman ruwan idan ruwan ya hadu da wayar, zai iya yin bindiga. Alhamulillahi, ya tabbatar mana da cewa, za su dauki mataki a kan haka.

Kafin zuwan ka yajin aikin likitoci da sauran ma’aika ya addabi asibiti, wanne hali ake ciki a yanzu ko kuma wanne goyon baya ma’aikatan ke baka don cimma burin farfado da Asibitin?

Gaskiya sai dai ince Alhamdulillahi, tunda nazo, na samu fahimta tsakani na da ma’aikata, don a ranar da nazo, na kira shugabanninsu na zauna dasu da kuma shugabannin sassasan Asibitin domin su san matsalar da Asibitin ke fuskanta na gaya masu baro-baro cewa gashi abinda nake ciki. Sai muka fara daga kasa don mu dora a kan halin da muka tsinci kan mu. Alhamdulillahi, ban samu wani matsala ko kalubale ko kuma barazana daga bangaren ma’aikata ba.

Ka yi maganar yin yarjejeniya da wani kamfani, wanne kira zaka yi ga sauran kamfanoni don hada hannu a ceto Asibitin daga halin da yake ciki a yanzu?

Kasan wannan neman tallafi yana da fadi sasai domin akwai wanda zaka samu daga gun kungiyoyi masu zaman kansu, dai-daikun mutane da kuma gun gwamnati wanda shi ne dauki dukkan wadannan hanyoyin na samun tallafin ai sai mutum yaga cewa, an gayra Asibitin, in ba haka ba, ba wanda zai dauki kudinsa ya sanya, shi yasa kudin da muke dashi ne muke zubawa don mu samu ko zamu kai matsayin daga sifili zuwa sama, in mun kai hakan, sai mu fara neman mutane ko kungiyoyi masu zaman kansu, ta haka za mu iya samun tallafi mai dorewa.

Akwai kiran da zaka yi ga alummar masarautar Zazzau?

Ba abinda zan ce ga alummar Zazzau in banda godiya domin sun yi hakuri sosai sun kuma ga yadda Asibitin nan yake, da aka nada ni kungiyoyi da dama sunzo don taya ni murna da yi min maraba suna kuma bani goyon baya. Lallai a kan haka nema Mai Martaba Sarkin Zazzau Dakta Shehu Idris ya fito ya yi magana a kan Asibitin, lallai muna godiya kwarai da gaske.

Wanne tabbaci za ka bai wa masu zuwa jinya Asibitin na cewa komai ya gyaru?

Alhamdulillahi, duk wanda ya zo Asibitin a cikin watanni hudu da suka shige, kuma yazo yau zaiga akwai banbanci, idan har akwai wata matsala da kaina nake zuwa dakin gaggawa na hadurra in duba  duk dare ko kuma sauran dakunan da aka kwantar da majin yata. Ina son in basu tabbaci da kwarin gwiwa, idan mutum baida lafiya ya zo wannan tsoron na in kazo Shika gidan mutuwa ne yanzu maganar ta wuce domin muna yin aiki tukuru don sauke nauyin da aka dora mana harda gudanar da bincike da ayyuka da bayar da horo kuma zamu ci gaba a kan hakan.

A karshe wanne sako kake dashi ga alummar ga al’umma gaba daya?

Sako na a gare su shi ne, bawai yan cikin garin Zariya kawai ba, dama wadanda suke zuwa daga waje na san cewar, Asibitin nan bana Zariya kawai bane, kuma bana ‘yan Arewa bane kawai, akwai mutane da dama da suke zuwa daga wurare daban daban, toh muna sanun matsala a kan lokacin da aka ware don zuwa ziyarar majinyata, daga karfe 4 na yamma zuwa karfe 6 na yamma daga Litinin zuwa juma’a, amma zaka ga mutane a manyan bas-bas suke shigowa a duk lokacin da suka ga dama, in an hana su, ya zama matsala, ko a ranar Juma’ar nan, mun fuskanci irin wannan matsalar, wani yana son ya chakawa likita kwalba, haka suka chakawa wani mai gadinmu wuka a cikin nan Asibitin saboda an nemi mtane su bika’idar da aka sanya. Yakamata mutune su dinga yin hakuri, domin abinda ya lalace da dadewa zai dauki kokaci kafin a gyra shi.

Su dinga kiyaye lokacin da aka ware don zuwa ziyara domin na daya, hakan zai bai wa ma’aikatanmu samun yin ayyukan su yadda ya dace, domin in aka zo aka cika dakin yaya za su iya yin aikin su yadda ya kamata, shima mai jinyar, ba zai samu ya huta ba. Kuma su sani cewa, nan Babban Asibitin Kwararru ne wannan ba karamin Asibiti bane, kuma sannan, bawai don kana fama da Maleriya sai ka taso kazo nan ba, akwai sauran Asibitocin mataki na karami kamar na nan Tudun Wada, suna da kwararrun ma’aikata da sauran su sai mutane su dinga zuwa can, nusamman don mu rage yawan cunkoso a wannan Asibitin yadda zamu samu damar duba wadanda suke da babbar bukata ta nusamman.

Farfesa Mun godiya

Nima na gode, kwarai da gaske

SendShareTweetShare
Previous Post

Sana’a Ce Babbar Hanyar Samun Ingantacciyar Rayuwa

Next Post

Mun Yi Farin Ciki Da Samun Nasarar Gwamna Ganduje—Bilya Asasco

RelatedPosts

Za A Kawar Da Ta’addanci A Jihar Xinjiang Sakamakon Wadata Da Zaman Karko

Za A Kawar Da Ta’addanci A Jihar Xinjiang Sakamakon Wadata Da Zaman Karko

by Bello Hamza
1 year ago
0

Babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG...

Tunawa Da Gwarzo Dakta Bala Yusuf Usman

Tunawa Da Gwarzo Dakta Bala Yusuf Usman

by Bello Hamza
2 years ago
0

Wakilimu ya yi takaitaccen bincike a kan rayuwa da gudummawar...

Rayuwar Mu A Yau Youth Awareness Association (Rayaas) Sokoto Chapter.

Rayuwar Mu A Yau Youth Awareness Association (Rayaas) Sokoto Chapter.

by Bello Hamza
2 years ago
0

Assalamu alaikum Editan LEADERSHIP A YAU LAHADI MALLAM BELLO HAMZA,...

Next Post
’Yan Mowa Da ’Yan Bora A Rukunin Kofin Zakarun Turai!

Mun Yi Farin Ciki Da Samun Nasarar Gwamna Ganduje—Bilya Asasco

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version