Ali Abubakar Sadiq" />

Mun Yi Watsi Da Umarnin Karatu (I)

A wancan makon da ya gabata hoton wata budurwa mai siyar da Awara a bakin titi a cikin birnin Kano wadda ke suyar awararta sannan ta na rike da littafi ta na karatu, ya karade shafin facebook tare da tofa albarkacin bakin mutane da dama. Cikin irin martini da wasu su ka bayar na cewa ba wani abin birgewa a cikin lamarin, saboda littafin soyayyar Hausa ta ke karantawa ya ja hankali na wajen yin wannan mukala domin kore irin wannan tunani.

Zan bada misalai da abubuwa da suka shafi rayuwata a matsayin hujja. Na farko dai tun ina dan karami aka kaimu makarantar kwana ta firamare a garin Roni, daya daga cikin kwaya biyu kacal da ake da su a wancan lokaci a fadin arewacin Najeriya. A wannan makaranta na fara karatun littafan hausa irinsu Magana Jari ce, Dare dubu da daya, Gandoki, Iliya Dan Mai Karfi da sauransu. Wannan ya bani damar gogewa wajen iya karatu da kuma sabo da shi.

Wani malaminmu inyamiri Mr. Ameachi ya hada gasar karatun hausa wadda na lashe kuma aka bani sulai bakwai, kudaden farko a rayuwata da na samu na kashin kaina. Wannan ya sa na dada jajircewa wajen karance-karance. Ina zuwa sakandare sai na fara karatun littafan turanci inda na rungumi littafan James Hardly Chase, yadda duk inda na ke sai ka ga wannan littafi tare da ni duk da cewa na sha tsangwama a lokuta kasancewar a bangon littafin akwai hotunan yan mata daga su sai dan kamfai. Karance karancen littafai na hausa da Turanci ya sa na sami gogewa a magana da rubutu a yaren hausa da na turanci, baya ga saka min shaukin karatu.

Na karanci fannin kimiyya a sakandare amma sakamakon faduwa a darasin Physics ya katse min burina na zama masani a fannin kimiyya abinda ya tilasta min canza layi yayin da na shiga jami’a. A jami’a sai na koma kan karatun hausa da sashen addinin musulunci abinda ya bude min sabon shafi saboda na fara yin nazarin Kur’ani maimaikon takararsa kawai. Cikin lokaci kankane na fahimci cewa shi Kur’ani ya na bukatar mai karanta shi ya zama mai bincike saboda ya tabo kowanne sashe na ilimi. Wannan dabi’a ta Kur’ani ita ce ta saka daular Abasiyawa ta yi shura a duniya a lokacin da musulunci yayi shaharar da ba’a taba gani ba a baya. Ilimin da na samu a nazarin Kur’ani da kuma na kimiyya ya bani damar yin zurfafan bincike yadda na rubuta littafai tare da makaloli iri-iri a wannan fanni na kimiyya da addini, yadda har daya daga cikin jami’o’i mafi girma a duniya, wato Jami’ar Cambridge da ke kasar Birtaniya ta karrama ni a shekarar 2008.

Ilimi shi ne ginshikin rayuwar Dan Adam kuma ba za ka iya samun ilimi ba har sai ka iya karatu kuma ka saba da yin karatun. Ni’imar karatu da rubutu ita ce ta banbanta Dan Adam da duk sauran dabbobi a wannan duniya domin sakamakon ta ne, mutane su ka iya neman ilimi su adana shi, sannan su yi amfani da shi da kuma yada shi. Duk wanda ya rayu tsawon shekaru hamsin da su ka gabata shaida ne kan yadda Dan Adam ya habaka fannonin ci gaba ta hanyar ingantar ilimai na fasaha da kimiyya. Abubuwan da aka kirkiro cikin wannan shekaru hamsin, ba wanda ya ke hasashen yiwuwarsu shekaru sama da dari da su ka gabata.

Alal hakika Musulunci shine ginshikin samar da ci gaban zamani wanda kasashen yamma su ka samar, kuma ya samo asali daga lokacin da a cikin kogo a wajen garin Makka, Annabi Muhammadu ya fara karbar wahayi daga ubangijinsa yayin da Jibrilu ya ce masa “Yi Karatu” inda annabi ya tambaye shi me zai karanta. Shin Jibrilu ya sanar da shi game da sallah, azumi ko zakka ne? A’a, ya umarce shi da ya karanta yadda Allah ya halicci mutum daga gudan jini, wato kai tsaye koyarwar farko ga manzo ita ce ta kudira da kimiyyar yadda Allah ya halitta mutum. An umarci annabi ya yi nazari da bincike wajen gane yadda Allah ya halicci mafificiyar halittarsa a doron kasa. Don haka a bayyane ya ke cewa umarnin farko a musulunci shine na neman ilimi kuma musamman ilimi na rayuwa da duk wani abu a doron kasa ko da kuwa shaidan ne, domin sai ka san yadda shedan ya ke kafin ka iya kaurace masa.

Neman ilimi a musulunci, sabanin sauran addinai ba aikin malamai kawai ba ne, kowanne mutum ya wajaba ya san daidai gwargwado na ilimi. Halifofon Abasiyawa, musamman Harun Al-Rashid da dansa Al-Mamun, sun yi rawar gani a tarihi yadda musulunci ya kai kokoluwar da bai taba kaiwa ba kuma su ka mamaye duniya ta wancan lokaci da karfin ilimi. A lokacinsu fannonin kimiyya, fasaha, falsafa, likitanci da sauransu sun habaka sakamakon sun bada damar bincike da nazari, kuma yawanci abubuwa na kimiyya sun samo asali daga irin wadancan bincike na daular musulunci. Harun Al-Rashid ya gina “Baitul-Hikma” (Gidan hikima) wurin da ya kasance cibiyar nazari da binciken kimiyya ta farko na kasa-da-kasa a tarihin duniya. Garin Bagadaza, wanda kakansa Khalifa Al-Mansur ya gina a gabar tekun Tigris, a karkashin mulkin Harun Al-Rashid ya zama birni mafi girma a duniya da cigaba wanda ke da littafan da babu irinsu a duniyar wancan lokaci kafin dakarun Hulagu Khan (jikan Ghengis Khan) ya kai wa garin Bagadaza hari a shekarar 1258 inda ya mamaye garin ya kuma kashe dubban daruruwan musulmi har da Khalifansu kuma ya sa aka kwashe littafan nan aka watsa su a kogin Tigris. Wasu masana tarihi sun ruwaito cewa sai da wannan kogi ya koma baki-kirin sakamakon daruruwan dubban littatafai da tawadar su ta wanke cikin kogin. Wannan hari na yan Mangoliya shi ya durkusar da daular musulunci a Gabas ta tsakiya wadda ba ta sake farfadowa ba.

Bayan kifar da yan gidan Umayya da daular Abasiyawa su ka yi, wani bangaren na su ya yi hijira inda su ka sake kokarin kafa daular a yankin Turai na yanzu, inda su ka mamaye zirin Iberia (inda kasar Portugal da Spain su ke a yanzu) suka kafa sabuwar daula da aka kira da daular Andalusiya. Wannan daula ta yi mulki a wannan waje na kimanin kusan shekaru dari takwas. A lokacin da ta ke ganiyarta, babban birnin wannan daula shine garin Cordoba, garin da ya zama mafi shahara a duniya, tamkar ka ce New York a yanzu. Wannan gari ya zama matattarar ilimi wadda sai dai a iya gwada ta da Bagadaza, domin a tsaikonta ta na da kimanin dakunan karatu da bincike sama da saba’in a lokacin da a gaba dayan turai babu dakin karatu na jama’a ko da guda. An fassara miliyoyin littafan Girkawa zuwa larabci a wannan gari, kama daga adabi, kimiyya, falsafa da sauransu. Dalibai sun yi ta barkowa daga Jamus, Ingila da Faransa domin kwankwadar ilimai daga wannan gari, domin babu inda za’a same shi a duniya a wancan lokaci idan ba Cordoba ba. Ba kawai a koyar da ilimin su ka tsaya ba, wannan daula ta samar da masana kimiyya da fasaha wadanda su ka habaka, a zahirance, yadda ake yin noman rani, tsaron garuruwa, gina jiragen ruwa yadda jiragen su na yaki su ka mamaye tekun Bahar Rum tare da kai hare-haren sojoji har cikin turai a kasashen Faransa da Bienna. Sun kirkiro sabbin hanyoyin kai hare-hare da makamai, da na tsarin gine-gine, yadda har a gobe masallacin Alhambara ke cikin tsarin gini da Dan Adam ya sanya cikin mafi kyau a tarihin gine-gine a duniya. A wannan gari aka fara tsarin Tsangaya, yadda kowanne masallaci ke da makaranta hade da shi wadda ake koyar da yayan talakawa ilimai. Daga wannan tsari na tsangaya aka samo kusan ilahirin tsarin jami’o’i na bangare-bangare, tsarin digiri na farko zuwa digirgir da kuma tsarin rigar da ake sawa lokacin kammala karatu (Academic gown) wadda asalinta daga alkyabba ne da rawani na manyan malamai. Hatta takardar rubutu, wadda aka fara kirkirarta kimanin shekaru dubu uku kafin zuwan annabi Isa a Misra, ta isa garin Makka a shekarar 707 AD sannan sai bayan shekaru dari hudu ta isa kasar Turai a shekarar 1109 ta hanyar wannan gari na Cordoba.

Exit mobile version