Connect with us

LABARAI

Muna Aiki Da Nijeriya Don Yakar Rashawa –Birtaniya

Published

on

Kasar Birtaniya ta bayyana cewa, tana aiki kafada da kafada da Nijeriya wajen yaki da cin hanci da rashawa ta hanyar samar da tallafin kayan aiki ga hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na Nijeriya. Babbar wakiliyar kasar Birtaniya a Majalisar Dinkin Duniya, Ambasada Karen Pierce, ta bayyana haka a wani taro na kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniyar da aka yi a kan yaki da cin hanci da rashawa, ta ce, kasashen biyu na aikin fadakar da jama’a a kan illar cin hanci da rashawa da kuma bukatar fallasa duk inda akyi wannan badakalar.

Ta kara da cewa, kasar Birtaniya babbar mai goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya ne a kan yaki da rashawa, ta ce kasar Birtaniya ta dauki nayin wani babban taron a kan yaki da cin hanci a garin Landa, tare da kudurin kara kaimin yaki da cin hanci a fadin duniya.

Pierce ta kuma ce, “Dawo da kaddarori na daga cikin manya manyan ginshikan yaki da cin hanci na duniya kuma yaa daga cikin kudurorin Majalisar Dinkin duniya.

“A shekarar 2017 mun dauki nauyin taron duniya kan dawo da kudaden da aka sata tare da kasar Amurka da Bankin Duniya da kuma kungiyar UNODC.

“Wannan hadakar ta taimaka wajen shirin dawo da kaddarori na fiye da Dala Miliyan 300 zuwa Nijeriya.

“Wani bangare na dokokin ya bayar da mahimmanci ga tallafin kayan aiki da musayar bayanai don samun nasara.

“Birtaniya na alfahari da hadakar da muke yi tare da kasashen duniya da dama, inda muke musayar bayanai masu mahimmanci da horar da jami’an kasashen.

“A Nijeriya mun samar da tallafi na musamman ga hukumomin dake yaki da cin hanci da rashawa a cikin gida da kuma kasashen waje da fadakar da jama’a a kan alfamun yaki da cin hanci da kuma ilarta.’’

Ambasadan ta kuma ce, abin takaicin shi ne babu wata kasa da ta tsira daga annobar cin hanci da rashawa, ya kjuma ce a na asarar Tiriliyoyin dala a duk shekara ga harkaokin cin hanci da rashawa. Pierce t ace, cin hanci da rashawa na nakasa ci gaban kaashe ta kuma gurbata aiyuukan gwamnati tare da haifar da rashin jituwa a tsakanin ‘yan kasa, ta ce a a shekarar 2003, tsohon sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Annan ya kwatanta cin hanci da rashawa a matsayin babbar annoba ga rayuwar dan adam.

Ta kuma yi nuni da cewa, cin hanci da rashawa na da dangantaka da rikice riicen da ake fama da shi a fadin duniya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: