Daga Muhammad Shafi’u Saleh, Yola
Wani taron Shugabannin Majalisun dokokin Jihohi Na Kasa (conference of State legislatures of Nigeria) ya yi amanna da rage karfin ikon shugabanni, kama daga matakin gwamnoni da shugaban kasa. Shugabannin majalisun sun ce yin haka zai dace da bukatun ‘yan Nijeriya.
Shugaban taron kuma Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Honarabul Isma’ila Abdulmumini, ya shaidawa manema labarai haka a Yola, bayan kammala taron na kwanaki biyu.
Honorabul Isma’ila ya ce; “Majalisun tarayya a kasar nan a shirye suke da su duba batun rage karfin ikon gwamnoni da shugaban kasa, domin zai dace da bukatun ’yan Nijeriya. Wannan taron yana mai bukatar majalisun tarayya da su yi dokar da zata mutunta ayyuka idan an amince da dokar”.
Ya ce, taron ya amince da majalisun jihohin a matsayinsu na masu wakiltar jama’a, za su gudanar da kuri’ar jin ra’ayoyin ‘yan Nijeriya ga duk abubuwan da zasu taimaka wajen kyautata rayuwar ‘yan kasar.