Muna Ayyukan Miliyoyin Kudi A Dukkan Mazabun karanar Hukumar Dala – Dan Isle

Daga IBRAHIM A MUHAMMAD,

Shugaban karamar Hukumar Dala, Hon Ibrahim dan Isle ya bayyana cewa bita da hukumar da’ar ma’aikata ta shirya wa Shugabannin kananan hukumomi da Kansiloli a Jihar Kano abune mai muhimmanci da zai kyautata ayyukansu.

Ya yi nuni da cewa dama akwai rashin cikakkiyar wayewa da wasu ba suda ita wajen cike fom na gabatar da kadarori duk wannan ana yi ne don kara sani a kan ka’doji da yakamata a cike takardun bayyana kadarori.

Ya ce, abune mai muhimmanci a samar da ofisoshi na irin wadannan hukumomi domin su zama kusa da mutane domin yanzu a Kano hukumar karafe-korafe da yaki da rashawa na Jihar Kano ne keda ofis a kasarnan hukumomi wannan ya taimaka Musu wajen saukaka ayyuka da wayar da kan al’umma wajen tuntubarsu.

Alhaji Ibrahim dan Isle ya ce, idan hukumar da’ar Ma’aikata za ta samar da ofisoshi a kananan hukumomi 44 zai taimaka wajen sake wayar da kan zabbabu dan hatta wanda ake muka ba su da cikakken ilimi me yakamata ayi da kudaden su samun irin wadannan hukumomi zai sa talakawa su gane cewa abinda ake so zababbe ya mallaka bai wuce albashinsa da alawus ba haka kansila wanda ya tsallake wannan ya wuce ka’ida dan haka talaka ba zai zo da neman abinda bai dace ba.

dan Isle ya ce, a matsayin sa na Shugaban karamar Dala cikin watanni takwas yayi ayyuka da dama na gina al’umma da ayyuka muhimmai ba inda ba shida aiki samada da biyu a dukkan mazabu 12 da suke a Dala. Yanzu haka akwai bayyuka da ake na Naira miliyan biyu-biyu a kowace mazaba a mazabar Gibirawa ma na Milyan Hudu ake.

Ya ce, yanzu dama da Gwamna ya basu na ayyuka suna yin aiki na milyan 33 a mazaba daya wani wurin na 20 akwai hanya da za a yi a Gibirawa da zai lashe Biliyan 57, akwai kyakkyawar fahimta da kansiloli da basu dama ta aikinsu a matsayinsu na yan majalisa.

Alhaji Ibrahim dan Isle ya yaba da irin goyon baya da hadin kai da kwamishinan kananan hukumom Alhaji Murtala Sule Garoi ke basu domin ya rikesu a matsayin Uba duk wani taimako yana basu dan cigaban karamar hukumar Dala.

Exit mobile version