A jiya Litinin ne wani mawaki mai suna, Charly Boy, ya shirya wata zanga-zanga a Abuja, inda aka bukaci shugaba Buhari ko dai ya koma aiki ko kuma ya sauka daga mukaminsa, saboda ya cika wata uku yana jinya a kasar Birtaniya, kamar yadda wasu ‘yan kasar suka bayyana..
Sai dai wata kungiya matasa ma su gangamin cigaba da mulkin Shugaba Buhari (Buhari Campaign Organisation) da ke yankin garin Ibadan babban birnin jihar Oyo, yayin da kungiyar ke gangamin cewa har yanzu su na tare da shugaba Buhari har zuwa zaben 2019.
Kungiyar ta kara da cewa, Duk da halin da Shugaban kasa ke ciki a birnin Landan muna tare da shi dari bisa dari kuma za goyi bayansa har zabe na gaba.