Muna Bukatar Aguiro Ya Dawo Wasa – Guardiola

Aguero

Kociyan kungiyar kwallon kafa Pep Guardiola ya ce lallai Manchester City tana bukatar Sergio Aguero da ya koma buga mata saboda a wannan lokacin suna bukatar kasancewarsa a cikin tawagar tasu sakamakon kwarewarsa.

Rabon da Manchester City ta zama ta daya a teburin gasar Ingila tun ranar 17 ga watan Agustan shekarar 2019 wanda hakan yasa aka fara hasashen cewa karsashin kungiyar ya fara disashewa a karkashin koyarwar Guardiola.

Dan kwallon tawagar Argentina ya buga wa Manchester City minti 141 a wasanni biyar a dukkan karawa a bana kuma ya yi minti 31 a karawar da Manchester City ta yi da West Ham United sai minti 24 ga watan Oktoba, ba buga karawar da Manchester City ta yi da Aston Billa ba ranar Laraba bayan da dan kwallon ya killace kansa, bayan da ya kamu da cutar korona.

Rashin Aguero a Manchester City ya bai wa Gabriel Jesus da Kebin de Bruyne da Ferran Torres da kuma Riyad Mahrez daukar alhakin ci wa kungiyar kwallaye kuma daga ranar 22 ga watan Disamba Manchester City ta ci kwallo 20 a wasa bakwai, ba tare da Aguero ba wanda ya zura kwallo 256 a kaka tara da rabi da ya yi a kungiyar.

Bugu da kari Manchester City wadda ta kai wasan Caraboa Cup bayan ta doke Manchester United ta yi wasanni 13 ba tare da kwallo ya shiga ragarta ba a wannan kakar duk da cewa a baya tayi kamfar kwallaye

A ranar Litinin ne dai kungiyar Fenerbahce ta kaddamar da Ozil a gaban ‘yan jarida bayan an dauki lokuta ana tattaunawa tsakanin kungiyoyin guda biyu kafin a amince da kulla yarjejeniyar a ranar Lahadi.

Exit mobile version