Daga Idris Umar, Zariya
A wata takardar manema labarai da shugaban kungiyar ya fitar a wannan satin takardar na nuna cewa ya kamata jam’iyyun siyasa su marawa irin su Nasiru Ahmed El-Rifa’i baya domin kawo karshen mulkin da cofafi keyi a kasa baki daya cewar Shuaibu Gomna.
Amb shuaibu Gomna, shugabane a majalisar nan ta matasa da ake kira NYMiP a jihar Kaduna muma shugaban ya cigaba da bayyana cewa, “Abu ne sananne cewa a yayin da tsari ya gurbace, to hakkin matasa ne a matsayinsu na wadanda kasar ta dogara da su su yi gyara. Sai dai abin takaici, su kansu matasan suna fuskantar matsalolin da gwamnatocin da ke cike da baragurbi da masu rashin sanin makamar aiki suka haifar.
“Wannan ne dai lokacin da ya kamata matasa su tashi tsaye domin shiga cikin gwamnati su shiga a dama da su a siyasa da abinda ya shafi yanke hukunce-hukunce a gwamnatance ba su kasance ‘yan amshin shata ba ga ‘yan siyasa.
“Duk da cewa an ga karuwar bukatar neman cigaba daga abubuwan da akan tura a kafofin sadarwar da matasa ke amfani da su domin ganin an dama da su a zabukan kananan hukumomi, musamman a nan jihar Kaduna, wanda kuma yunkuri ne wanda ya kamata a yaba da shi, ana bukatar jam’iyyu su taimakawa matasan da suka nuna wannan niyyar.
“Gaskiya dai zage-zagen juna da binciken kwakwaf ga juna bai kaimu ko’ina ba kuma abun mamaki ne a ce zanga-zanga da kokari a siyasance ba su kaimu ko’ina ba bayan an kaddamar da kamfe din Not Too Young To Run da kuma #Endsars, da kuma wasu abubuwan da dama da aka yi nasara a kansu ta hanyar zanga-zanga. Maganganun da mai girma gwamna El Rufai ya yi na jarumtane kuma sun nuna irin soyayyarsa ga matasa kuma ya kamata su zama abin koyi ga sauran shugabanni da kuma jam’iyyun siyasa. Ya kamata a rungumi matasa a kuma karbesu domin sune mafari.”
Shugaban ya kuma jinjinawa shugabancin APC domin fara sabunta rijista da ta yi na katin shaidar ‘yan jam’iyya, wanda ya ba matasa da dama damar taka rawa a siyasa. Muna ma kira ga sauran jam’iyyu da su yi koyi da ayyukan APC din, musamman PDP itama ta samar da hanyar katin zama dan jam’iyya domin a dama da matasa a siyasa, muna ma so mu roke su da su fito da hanyoyin bayyana manufofi da muhawara ga ‘yan takara domin gujewa gurbatattun ‘yan siyasa da ke wahalar da yanayin siyasar kasarmu.
Shugabancin NYMiP da ke da goyon bayan cigaban matasa, wayar da kan matasa a siyasa da a gwamnatance za ta cigaba da tabbatar da cewa an dama da matasa a wannan lokaci na.siyasa a jihohi 36 da ke kasar nan a wani yunkuri ko hobbasan mambobinmu da ke jihohi.’