Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home NOMA

Muna Bukatar Takin Zamani –Manoman Rogo A Kwara

by Muhammad
January 21, 2021
in NOMA
3 min read
Rogo
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Manoman Rogo a jihar Kwara sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta taimaka masu da takin zamani da kuma ingantaccen irin na Rogo tare da taimaka masu da kayan noman rani.

Akasarin alummar mazabar Lafiagi ta uku a cikin karamar hukumar Edu a jihar Kwara, amfi sanin su da noman Rogo, inda Yankunna su ne, Zambufu, Gale, Masha, Guye, Gbugbu da uka sauransu.

An ruwaito cewa, wasu alumomin dake cikin jihar ta Kawara, wasu maomna sun bayyana jin tsron sun a cewar, fannin na noma da suka gada kaka da kakakani yana fuskantar matukar barazana.

Alal misali, a kan hanyar zuwa shalkwatar Zambufu zuwa mazabar Gbale cike take da ramuka, inda kuma zaizayar kasa ta fara cinye hanyar hakan kuma ya sa manoman suke fusktar matsalar jigilar amfanin gonaar su dag suka shuka zuwa cikin gari.

Mallam Ibrahim Gbale ya kuma koka akan yadda Fulani makiyya suka yawan kai masu hari, inda ya ce, hakan yana kuma kara haifar da tsoro da fargaba a tsakanin manoman a yankin, inda ya kara da cewa, Jijiyar Rogo na kai wa shedara a daya da rabi kafin ta rika, amma abin takaici a lokacin rani, Fulani makiyaya suka mamaye mana gonakan mu su kuma cinye mana Rogon da muka shuka.

A cewar Mallam Gbale mazauna yankin da kuma wasu da muke yin makwabtaka dasu kusan manoma su 1,000 manoman Rogo ne, inda suke samar da tan-tan masu yawa a duk shekara, inda kuma ya koka kan cewar, basa samun wani dauki daga gun gwamnati domin an jima da yin watsi da alummar mu, domin idan ka lura hanyar da muke tafiya akai duk ta lalace.

Ya sanar da cewa, jigilar amfanin gona daga gonakan mu zuwa kasuwanni wani babban jidali ne saboda yadda hanyar dta lalace kuma masu motocin haya basa son bin hanyoyin saboda yadda suka lalace, inda ya ci gaba da cewa, sa, hakan yana zamo wa matukar wuya wajen kai amfanin gonar mu zuwa kasuwannin Tsaragi and Gbugbu.

Shi ma wani manomin na rogo Dauda Mohammed a yankin ya sanar da cewa, ginakai sun lalace saboda matsalar zaizayar kasa da kuma rikicin manoma da makiyaya a yankin yana jefa mu a cikin matsala.

Ya ci gaba da cewa, a yanzu ba a iya noma Rogo a gonakan mu ba tare dam un zuba takin zamani ba wanda abin bah aka yake a baya ba kuma mu a nan jihar Kwara, ba mu samun wani taimako na kayan aikin noma daga gun gwamnati, inda ya kara da cewa, dukkan iya kokarin da akayi don a kawo karshen rikici tsakanin manoma da makiya a yankin, hakan ya faskara, domin Fulani makiyaya suna mamaye gonakanmu suyi ma na barna na Rogon da muka shuka.

Ya yi nuni da cewa, in har ba a kawo karashen hakan ba, za’a iya fuskantar matsalar karancin abinci a yankin.

Wani mai fada aji a cikin kauyen Issa Ndade ya ce, manoma 300 ne ke yin noman Rogo a kauyen kuma aikin noma shine mu ka gada kaka da kakanni, inda ya ce gaba dada cewa, a yanzu, mu na da kada kusan 600 da ake noma Rogo kuma mafi yawancin alummar kauyen harda mata manoman Rogo ne.

Shi ma wani manomin a yankin Ya’Nda Mohammed ya ce, babbar matsalar da su ke fuskabta it ace ta yadda zamu yi jigilar amnanin gonar mu zuwa kasuwa saboda yadda hanyar ta lalace, inda kara da cewa saboda hakan muna kasha kudi da yawa wajen jigilar ta amfanin gona zuwa kodai gidajen mu don adana wa ko kuma kaiwa kasuwa don siyarwa.

Manoman sun kuma yi kira ga gwamnatin jihar ta Kwara da ta samar masu da masana’antar sarrafa Rogo, musamman don su magance asarra da suke tabkawa a lokacin yin girbin na Rogo.

Shi ma wani manomain Rogo Dauda Mohammed ya sanar da cewa, samar masu da kayan sarrafa Rogon zai sanya sana’ar su ta kara bunkasa kuma hakan zai kara janyo hankalin matasa su rungumi fannin na noman Rogo.

Dauda Mohammed ya kuma koma kan yadda ake samun rikicin manona da Fulani makiyya a yankin, a saboda hakan, muna kira ga gawamnatin jihar da ta yi dukkan mai yuwa wajen kawo karashen rikicin domin rikicin na kara karyawa manoma kwarin gwiwa a yankin, inda kuma . ya sanar da cewa, dukkan iya kokarin mu da muka yin a kawo karashen rikicin a tsakanin mu da fulani makiyaya hakan yaci tura.

SendShareTweetShare
Previous Post

Kananan Manoma Sun Bukaci Bashi Daga CBN

Next Post

Talakawan Nijeriya Miliyan 24.3 Sun Samu Tallafin Naira 5,000 Kowanne – Ministar Jinkai

RelatedPosts

Kwakwar Manja

An Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Noman Kwakwar Manja

by Muhammad
3 hours ago
0

Kungiyar masu noman kwakwar manja ta kasa  OPGAN ta gudanar da...

Karo

Gwamnatin Tarayya Za Ta Cigaba Da Samar Da Ingantattun Irin Karo – Minista Shehuri

by Muhammad
1 day ago
0

Gwamnatin Tarayya ta shelanta cewa, za ta ci gaba da...

Karo

Yadda Za A Kara Fadada Noman Karo A Nijeriya -UNCTAD

by Muhammad
3 days ago
0

Daga Abubakar Abba, Taron sashen Majalisar Dinkin Duniya kan kasuwanci...

Next Post
Talakawan Nijeriya

Talakawan Nijeriya Miliyan 24.3 Sun Samu Tallafin Naira 5,000 Kowanne – Ministar Jinkai

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version