Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mikel Arteta, ya tabbatar da cewa shugabannin kungiyar suna ci gaba da Magana akan makomar dan wasa Mesut Ozil wanda yake shirin barin Arsenal a wannan watan na Janairu.
Arteta ya bayyana haka ne bayan tashi daga wasa da Arsenal ta buga 0-0 da kungyar kwallon kafa ta Crystal Palace a wani kwantan wasa da suka fafata a ranar Alhamis sai dai bai fayyace kungiyar da dan wasan zai koma ba.
Rabon Ozil da buga wa Arsenal wasa tun a cikin watan Maris na shekarar 2019 duk da cewa ya sha nanata cewa yana jin lafiya kamar ingarman doki, kuma a shirye yake ya yi wasa amma Arteta baya amfani dashi.
Tsohon dan wasan na Real Madrid ya fito sosai a dandalin sada zumunta tun lokacin da aka daina ganinsa a filin kwallo, inda har a rana Litinin da ta gabata ya dinga amsa tambayoyin masu bibiyansa a Twitter.
Sai dai yayin da har yanzu ake dakon fayyace makomarsa a Arsenal, Mesut Ozil ya ce baya nadamar kulla yarjejeniya da kungiyar da kawo yanzu ya shafe akalla shekaru 7 tare da ita duk da a yanzu baya buga wasa
A shekarar 2013 Ozil ya sauya sheka daga Real Madrid zuwa Arsenal kan kudi fam miliyan 42 da rabi, inda kuma a tsawon lokacin da suke tare ya taimakawa kungiyar wajen lashe kofunan FA guda uku, da na Community Shield guda daya, haka zalika ya lashe kyautar dan wasa mafi kwazo a kakar wasa ta 2015 zuwa 2016.