Mai koyarwa Ole Gunnar Solskjaer ya ce, Manchester United tana da sarari da kudin da za ta karfafa kungiyar a wasannin bana ta hanyar sayan ‘yan wasan da take ganin idan ta kawosu zasu taimaka mata wajen samun nasara.
Manchester United tana mataki na 12 a kasan teburi da tazarar maki biyu tsakaninta da ‘yan ukun karshe, kuma Liverpool ta daya ta bai wa Manchester United tazarar maki 15 bayan buga wasan sati na takwas a bana.
Ranar Lahadi ne Manchester United za ta karbi bakuncin Liverpool a wasan mako na tara a gasar cin kofin firimiya da za su fafata a bana sai dai mahukuntan Manchester United suna shan suka kan kasa taka rawar gani da kungiyar ke yi a wasannin firimiya na bana.
Manchester United ta kashe fam miliyan 145 wajen sayo dan wasan baya Harry Maguire da Aaron Wan Bissaka da kuma Daniel James, kuma Solskjaer ya ce akwai kudi a kasa da zai karo wasu a watan Janairu.
Solskjaer ya c e akwai jan aiki a gaban United na takawa Liverpool burki a shirin da take na lashe kofin firimiya bana wanda rabonta da shi tun shekara ta 1990 sai dai ya bayyana cewa zasuyi iya kokarinsu domin bawa duniya mamaki.
Kocin ya kara da cewar kwantiragin shekara uku ya sa hannu a wajen shugabannin kungiyar, saboda haka suna da shiri na dawo da martabar kungiyar a fanni kwallon kafa kuma akwai kudi a kasa domin sayan manyan ‘yan wasa.