Abba Ibrahim Wada">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home WASANNI

Muna Da Kudin Sayen Sababbin ’Yan Wasa – Solkjaer

by Abba Ibrahim Wada
February 15, 2021
in WASANNI
2 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Ole Gunner Solkjaer ya bayyana cewa shugabannin kungiyar sun shirya kashe kudi wajen sayan sababbin ‘yan wasa kuma ko da yaushe a shirye suke su bayar da kudi domin sayan ‘yan wasa a kokarin da sukeyi na gina kungiyar kuma ya bayyana cewa zasu shiga kasuwa domin kara karfi.

A watan daya gabate ne rahotanni suka tabbatar da cewar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United za ta sayar da dan wasanta na tsakiya, Paul Pogba mai shekara 27 a duniya a karshen kakar wasa ta bana bayan ya tabbatar da cewa ba zai saka hannu kan sabuwar yarjejeniya ba a kungiyar.
Wannan na zuwa ne duk da cewa a ‘yan kwanakin nan tauraruwar dan wasan tana haskawa inda a wasan da kungiyar ta fafata na karshe-karshe ya bayar da mamaki sosai har aka fara rade radin cewa zai iya ci gaba da zaman kungiyar kafin yaji ciwo a wasan kungiyar data buga da Everton a satin daya gabata.
Har wa yau, Manachester United din ta rasa abin yi game da dan wasan Ingila da Dortmund, Jadon Sancho mai shekara 20, yayin da Ole Gunnar Solskjaer ya fi son Erling Braut Haaland na Dortmund din mai shekara 20 shi ma.
Sai dai abune mai wahala kungiyar Dortmund ta sayar da dan wasa Haaland kuma dole ne kungiyar ta dage akan dan wasan duba da yadda manyan kungiyoyi irinsu Real Madrid da Barcelona da Bayern Munchen suke bibiyar matashin dan wasan dan kasar Norway.
Sannan United din tana ci gaba da bibiyar dan wasan gaba na kungiyar Aston billa, Jack Grealish, wanda kungiyar ta nema a kwanakin baya amma cinikin bai samu ba yayinda ake ganin za’a koma ci gaba da maganar a karshen kakar wasa.
Solkjaer ya bayyana cewa akwai kudi a kungiyar kuma idan suka samu dan wasan da zaiyi daidai ba muradun kungiyar za su saya ko nawa ne domin daukarsa sai dai ya ce dole ne su nutsu saboda ba za su kashe kudi a inda bai kamata ba.

SendShareTweetShare
Previous Post

Gwamnatin Tarayya Na Da Kwarin Gwiwar Samun Haraji Mai Yawa A 2021

Next Post

Mun Hakura Da Lashe Gasar Firimiya – Klopp

RelatedPosts

Atletico

Za A Yi Kare Jini Biri Jini Tsakanin Real Madrid Da Atletico Gobe

by Abba Ibrahim Wada
10 hours ago
0

A ranar Lahadi ne Real Madrid za ta ziyarci filin...

Bale

Real Madrid Ce Kawai Zata Fayyace Makomar Gareth Bale -Mourinho

by Abba Ibrahim Wada
10 hours ago
0

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Jose Mouinho ya ce,...

Sevilla

Daman Nasan Muna Da Nasara A Kan Sevilla -Messi

by Abba Ibrahim Wada
10 hours ago
0

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Leonel Messi, ya...

Next Post
klopp

Mun Hakura Da Lashe Gasar Firimiya – Klopp

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version