Muna Da Kyakkyawar Fahimta Da Hukumar Kasuwar Abubakar Rimi – Shugaban Dattawan Kasuwar

Rimi

Daga Ibrahim Muhammad,

An bayyana cewa, akwai kyakkyawar dangantaka ta fahimta a tsakanin hukimar gudanarwa ta kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi, wacce aka fi sani da kasuwar Sabon Gari da ‘yan kasuwa dake gudanar da harkokinsu a kasuwar.

Shugaban Dattawan Kasuwar, Alhaji Ibrahim Danyaro ne ya bayyana hakan a zantawars da wakilinmu cikin makon nan.

Ya yi nuni da cewa a kwanakin baya lokacin da Hukumar kasuwar ta kawo maganar karin kudi na rumfuna da sabunta takardu da duba suka ga kudin sun yi yawa ga ‘yan kasuwar, musamman duba da yanayin da ake ciki, don haka suka koka wa Gwamnati akai.

Alhaji Ibrahim Danyaro ya kara da cewa a matsayinsu na ‘yan kasuwa sun kai kuka ga wanda abin ya shafa, wato Hukuma ta nuna musu cewa karin ya yi musu tsada.

Ya ce, akwai kuma wasu manyan Dattawa a kano da suka taimaka musu suka sanya baki kan lamarin, har aka sami fahintar juna tsakanin ‘yan kasuwar da Hukumar, aka rage musu kudaden da za su biya.

Alhaji Ibrahim Danyaro ya ce sakamakon wannan fahimtar juna, an sami sauki matuka na ragin kudaden da za su biya daga N1,000,000, kudin sabunta haya ya dawo N200,000. Sai kuma kudin shekara da Hukumar Kasuwa tace za a biya N500,000, an sami ragi, yanzu za a biya N50,000.

Alhaji Ibrahim Danyaro ya ce game da takaddamar da ake yi tsakanin wasu daga ‘yan kasuwar na Muhammadu Abubakar Rimi da Hukumar kasuwar kan runfuna da Hukumar ke neman ta tashesu, suna fata dukkan bangarorin za a sami fahimtar juna a sami maslaha a tsakani a warware matsalar cikin mutuntaka don ci gaban kasuwar da al’umma baki daya.

 

 

Exit mobile version