Abba Ibrahim Wada">

Muna Da Matsalar Zura Kwallo A Raga – Solkjaer

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Ole Gunner Solkjaer, ya bayyana cewa kalubalen da kungiyarsa take fuskanta a wannan lokaci shine na zura kwallo a raga kuma yana fatan zai samu damar shawo kan matsalar a wasannin gaba an kungiyar.

kalubalen Manchester United na lashe kofin Premier ya kara gamuwa da cikas a cikin kwanaki hudu inda suka rike juna da Arsenal duk da cewa kowacce kungiya tayi kokarin zura kwallo a raga.
Manchester United ta barar da damar darewa tebur bayan ta sha kashi ci 2-1 a tsakiyar mako a hannun kungiyar kwallon kafa ta Sheffield United, kuma yanzu ta yi barin maki biyu bayan tashi babu ci a filin wasan Arsenal wato Fly Emirates.
Yanzu maki uku Manchester City da ke saman tebur ta ba takwararta Manchester United sannan kuma maki shida ne tsakanin Arsenal da hudun farko a tebur a maki daya da ta samu a wasanta da Manchester United.
Manchester United ta kasa doke manyan kungiyoyin Premier League Manchester City da Liberpool da Tottenham da Chelsea ko Arsenal a Premier a bana wanda hakan ya nuna gazawar kungiyar sannan idan akayi la’akari da kakar data gabata kungiyar ta doke manyan kungiyoyi.

Exit mobile version