Muna Farin Ciki Da Nasarorin Da Kasuwar Mile 12 Ta Ke Samu

Daga Bala Kukkuru Legas,

Babban shugaban kasuwar mile 12 Intanashinal maket a Legas, Alhaji Shehu Usman Jibirin Samfam Dallatun EGBALAND Abeokuta ta jihar Ogun ya bayyana cewar shi da dattawan kasuwar Mile 12 Intanashinal maket da sauran al’umma wadan da suke gudanar da harkokin kasuwanci a cikin kasuwar suna cike da farin ciki tare da nuna murnar su a game da nasarorin da kasuwar take samu a kowanne lokaci.

Babban Shugaban kasuwar, Alhaji Shehu Usman Samfam ya yi wannan tsokaci ne a jawabinsa na maraba da manyan baki a wajan taron walimar yaye dalibai na makarantar Tazkyya Arabik schools wanda ya gudana a bakin kasuwar ‘yan tattasai dake unguwar Mile 12 Legas a ranar Lahadin da ta gabata.

Shehu Usman Samfam ya cigaba da cewa lallai shida dattawan kasuwar da sauran al’umma wadanda suke gudanar da harkokin kasuwancin daban daban a cikin kasuwar ta Mile 12 suna cike da farin ciki matukar gaske a game da wadannan nasarorin da suke samu a wajen jagorancin kasuwar da al’ummar cikin ta baki daya, ya ce kadan daga cikin wadannan nasarori sun hada samun zaman lafiya da hadin kan al’umma da gyaran kasuwar da tsaftaceta da samar da guraben kasuwanci ga al’ummar da samun gudummawa tare da amincema juna.

Ya kuma yaba wa shugabannin bangarorn kasuwa da suka hada da Alhaji Isa Mohammed mai shinkafa da tsohon shugaban kasuwar Alhaji Haruna Mohammed Tamarke da Alhaji Habu Paki garkuwan paki da Alhaji Abdulwahab tsoho babangida sauran sun hada da Alhaji Abdullahi burama da Alhaji sani na mowa da tsohon sakafaren kasuwar Alhaji Wada Yaro Kiru da dai sauran makamantansu.

Exit mobile version