Muna Fuskantar Kalubale A Bangaren Binciken Da Muke Gabatarwa

Bincike

Daga Idris Umar,

Daya daga cikin shugabannin Cibiyar Binciken Habaka Dimokuradiyya (CEDDERT), Farfasa Muhammad Mustapha Gwadabe ya bayyana cewa suna fuskantar kalubale a bangaren binciken da suke gudanarwa. Ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai.

Wannan cibiya ce da ta dukufa wajen bayar da tabbatacen rahoto a kan bambancin almajiranci da kuma bara a fadin Nijeriya. Cibiyar dai ta shahara wajen gudanar da bincike a bangarori da dama musamman a bangaren ilmi da tsaro da harkokin yau da kullun.

Cibiyar ta zama gagara misali a kan gudanar da bicike a kowani bangare a gida Nijeriya da kasashen ketare. Tuni cibiyar ta mallaki rajistanta a gida da waje don taimaka wa al’umar Nijeriya. Marigayi Dakta MD Yusuf daga Jihar Katsina da Marigayi Dakta Bala Usman suka kafa wannan cibiyar tun a shekarar 1992, domin kawo wa wannan kasa ci gaba ta kowani fanni musamman a bagaren dimokuradiyya.

A yanzun kuwa wasu bayin Allah ne da suka tsotsi ilmin daga garesu suke jan ragamar wannan cibiyar don taimakawa.

Exit mobile version