Daga Abdullahi Muhammad Sheka,
An jinjina wa kokarin ‘yan uwa, jami’an tsaro, ‘yan Kasuwar Kantin kwari da kafatanin jama’a da suka tsunduma cikin addu’o’i da kuma ‘yan Kasuwar mu na kantin kwari wadanda suka bayar da gudunmawar kudade, da uwa Uba ‘yan uwa da dangin wadanda akayi garkuwar dasu, wadanda tare da su muka yi ta fadi tashi har Allah ya kubotoana da jama’ar mu, muna Godiya kwarai da gaske.
Wannan jawabin ya fito daga bakin kakakin kungiyar ‘yan Kasuwar Kantin kwari, Ambasada Mansur Haruna Dandago lokacin da yake yiwa LEADERSHIP Ayau karin haske kan batun garkuwar da skayi da wasu ‘yan kasuwar kantin kwari da suke kan hanyarsu ta zuwa garin Onicha domin sayayyar kaya.
Dandago yace babu shakka ‘yan kasuwar Kantin kwari da kafatanin jami’ar Jihar Kano sun girgiza matuka bisa wannan al’amari wanda muka dauka a matsayin wata jarrabawa daga Allah. Yace babu shakka an kassara wadannan ‘yan uwa namu, an dukusar da harkokin kasuwancinsu, sannan an wahalartar dasu matuka, wannan tasa dole yanzu sai an sake kallon yadda za’a taimaka domin wadannan bayin su samu farfadowa daga mummunan halin da aka jefa su a ciki.
Kakakin kungiyar ‘yan Kasuwar Kantin kwari Ambasada Mansur Haruna Dandago ya kuma mika irin wannan sakon godiya ga Malamai attajirai, ‘yan siyasa bisa nuna damuwarsu Kan abinda ya samu ‘yan Kasuwa, musamman yadda aka tsunduma cikin addu’o’i da saukokin Alkur’ani mai girma a kafatanin masallatan Kasuwar tamuai albarka, mun gode Kwarai. Inji Haruna Dandago.