Abba Ibrahim Wada" />

Muna Goyon Bayan Conte Dari Bisa Dari, Inji Hazard

Eden Hazard dan wasan kungiyar Chelsea ya ce a iya saninsa ba ya jin akwai wani dan wasa a kungiyar din da ke adawa da mai koyar day an wasan kungiyar Antonio Conte.
Wannan na zuwa a yayin da wasu ke ganin sakamakon wasannin da Chelsea za ta buga da Barcelona a gasar zakarun Turai da kuma haduwarta da Manchester United a ranar lahadi a gasar firimiya su za su tantance makomar Antonio Conte.
Amma Hazard ya ce suna bayan kocinsu, kuma abin da suka sa a gaba shi ne darewa saman tebur tare da doke Barcelona.
Chelsea dai ta sha kashi ci 4-1 a gidan Watford a gasar firimiya, kafin ta huce a kan West Brom, nasarar da ta ba ta haurowa matsayi na hudu tebur.
Chelsea ta kai zagayen kusa dana kusa dana karshe bayan ta doke Hull City 4-0 a gasar kofin kalubale na FA da suka fafata a ranar Juma’ar data gabata.
Yanzu kuma Chelsea na shirin kai ziyara kungiyar kwallon kafa ta Manchester United karawar farko dai Chelsea tasamu nasara akan United daci 1-0 ta hannun dan wasa Albaro Morata.

Exit mobile version